Mawallafin jaridun Manhaja da Blueprint, Mohammed Idris Malagi, ya yi alhinin rasuwar Janar Wushishi

Daga WAKILINMU

Shugaban kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya dangane da rasuwar tsohon Hafsan Hafsoshin Soja, Janar Mohammed Inuwa Wushishi.

Alhaji Mohammed, wanda shi ne Kakakin Nupe, ya miƙa saƙon ta’aziyyar tasa musamman ga Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani-Bello, da ɗaukacin al’ummar Wushishi, Masarautar Kwantagora, jama’ar jihar, da Rundunar Sojojin Nijeriya a kan rasuwar ta Janar Wushishi, wanda ya riƙe muƙamin Hafsan Hafsoshin Sojan Nijeriya a tsakanin Oktoba 1981 zuwa Oktoba 1983.

A saƙon ta’aziyyar da ya aika a ranar Lahadi, Alhaji Mohammed Malagi ya bayyana mamacin a matsayin dattijon kirki wanda ya yi amfani da aikin sojan da ya yi cikin martaba da kuma hikimomin sa na kasuwanci ya ƙarfafa wa ‘yan Nijeriya daban-daban gwiwa wajen neman na kan su.

Ya ce, “Janar Wushishi ya na daga cikin manyan hafsoshin soja da su ka yi yaƙi domin tabbatar da haɗin kan Nijeriya, kuma ya tsaya tsayin daka a kan wannan ƙudirin na ganin haɗin kan ƙasa da dunƙulewar jama’a a duk tsawon rayuwar sa.

“Abu ne mai wahala a ce mu da mu ke a wannan zamanin ba mu amfana daga koyon halaye nagari irin na Janar Wushishi da sa’o’in sa ba wajen ciyar da batun haɗin kan Nijeriya ta zama ƙasa ɗaya.”

Mawallafin jaridun, wanda kuma shi ne shugaban gidan rediyon ‘We FM’ da ke Abuja, ya ƙara da cewa ya yi alhini matuƙa kan wannan rashi da aka yi, to amma ya karɓi ƙaddara musamman ganin cewa Janar Wushishi ya bar ababen da miliyoyin ‘yan Nijeriya za su ci gaba da koyi da su har abada.

Alhaji Mohammed Idris Malagi ya roƙi Allah subhanahu wa ta’ala da ya yafe dukkan kurakuran mamacin kuma ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi.

Haka kuma ya ba al’ummar Wushishi da Masarautar Kwantagora da jama’ar Neja da Rundunar Sojojin Nijeriya da ma ɗaukacin ‘yan Nijeriya haƙurin jure wannan babban rashi.

Shi dai Janar Wushishi, Allah ya yi masa rasuwa ne a ranar Asabar, 4 ga Disamba, 2021, a wani asibiti da ke birnin London.

Ya rasu ya na da shekara 81 kuma ya bar matar sa ɗaya, Hajiya Kande Inuwa Wushishi, da ‘ya’yan su guda bakwai.