Daga BASHIR ISAH
A Lahadin da ta gabata rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da mutuwar wasu yara su takwas waɗanda cikin kuskure suka kulle kansu cikin wata tsohuwar mota da ke ajiye a gefe a lokacin da suke wasa a kan hanyar Adelayo, Agunlayo, Jah Michael, kusa da yankin Magbon a Badagry.
Sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Legas, Adekunle Ajisebutu ya fitar, ta nuna ibtila’in ya auku ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Ajisebutu ya bayyana cewa, bayan da aka gano gawarwakin yaran an kwashe su zuwa ɗakin adana gawarwaki na Babban Asibitin Badagry domin gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwar yaran.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya da ya bibiyi lamarin ya ce, an gano yaran ne a mace cikin tsohuwar motar da ke ajiye a ƙofar gidan mai ita.
Jami’in ya ce rahoton da suka samu kan lamarin ya sanya Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Hakeem Odumosu, ya bada umarnin a gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiyar al’amari.
Bayanan manema labarai sun nuna tsohuwar motar da aka gano yaran a cikinta mallakar wani tsohon ma’aikacin Jami’ar Jihar Legas ne wanda a yanzu ba ya raye.
Wata majiya ta ce yaran sun buɗe motar ne da ƙarfin tsiya sannan suka shiga suka kulle kansu ba tare da wani ya san halin da suke ciki ba wanda daga bisani rashin iskar da za su shaƙa ya yi ajalinsu.
Majiyar ta ci gaba da cewa, lamarin ba shi da alaƙa da harkar satar mutane ko makamancin haka, ƙaddara ce kawai.
Dr. Tunde Bakare wanda shi ne shugaban Babban Asibitin Badagry, ya faɗa wa NAN cewa a mace aka zo da yaran asibiti.
Bakare ya ce: “Ko da muka buƙaci su bar mana gawarwakin su tafi don mu gudanar da bincike a kansu, sai wani malami da ya taho tare da su ya ƙi amincewa da hakan tare da cewa, kada jana’izar yaran ta wuce ranar Asabar.
“Ganin ɗan sandan da aka kawo gawarwakin tare da shi ya goyi bayan malamin hakan ya sa muka miƙa musu yaran.”