An yi addu’o’i na musamman ga Marigayi Bashir Ado a masallacin Gwammaja

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Al’ummar unguwar Gwammaja sun bayyana marigayi shugaban kwamitin amintattu na Masallacin Ihya’ussunnah da ke rukunin gidajen ‘yan majalisu, Alhaji Bashir Ado, wanda Allah Ya karɓi ransa a makon ƙarshe kafin watan Azumin Ramadan da ya gabata, a matsayin mutum mai gaskiya, riƙon amana, haƙuri da son zaman lafiya, tare da irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban masallacin.

An bayyana hakan ne a yayin wani taron addu’o’i na musamman da aka gudanar domin yi wa marigayin fatan rahama. Babban Limamin masallacin Gwammaja, Malam Lawan Abubakar Gwauron Maje, ne ya jagoranci addu’ar, inda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙoƙarin sada zumunci da hidima ga addinin Musulunci. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya yafe masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna.

Malam Lawan Gwauron Maje ya kuma yaba da irin gudummawar da wani jigo a unguwar Gwammaja, Alhaji Bashir Ibrahim Gwammaja, ke bayarwa, musamman yadda yake ɗaukar nauyin tafsirin Alƙur’ani a duk shekara a watan Ramadan, tare da kulawa da bunƙasa harkokin addini da tallafa wa marasa ƙarfi.

Ya yi kira ga masu hali da su yi koyi da halin kyautatawa da taimakon al’umma irin na Alhaji Bashir Ibrahim Gwammaja, yana mai jaddada cewa hakan na daga cikin abubuwan da addinin Musulunci ke ƙarfafawa.

Taron addu’ar ya samu halartar manyan mutane da dama daga unguwar Gwammaja, ciki har da Alhaji Bashir Ibrahim Gwammaja, Alhaji Ado Ya’u, Alhaji Ashiru Garun Ali, Abubakar Ala da sauran jama’a.

Haka kuma al’ummar unguwar sun yaba da irin ƙoƙarin da Alhaji Bashir Ibrahim tare da ‘ya’yansa, Alhaji Isma’il Bashir da Ahmad Bashir, ke yi wajen ɗaukar nauyin tafsirin Alƙur’ani da Malam Mubarak Lawan Gwauron Maje ke gabatarwa, yayin da Malam Abdulrazaƙ Lawan ke jan baƙi a cikin watan Ramadan a Masallacin Ihya’ussunnah.

By ukarofi