An yi garkuwa da basarake da iyalansa a Kaduna

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga a jihar Kaduna sun kai hari a masarautar ƙaramar hukumar Kajuru, inda su ka sace sarkin garin, Alhaji Alhassan Adamu da wasu daga cikin iyalansa.

An sace Sarkin tare da iyalan su 13 a harin da ‘yan bindigar suka kai da tsakar daren Lahadi.

Binciken Manhaja ya gano an sace Sarkin mai shekara 85 tare da matansa uku, jikokinsa biyu, ma’aikatansa uku da kuma ƙarin mutum biyar.

Bayanai sun nuna cewa Sarkin ya gudanar da taro ranar Juma’a a kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa.

Wannan lamari na faruwa ne ƙasa da mako guda da sace ɗaliban Makarantar Sakandaren Bethel Baptist fiye da 100 da ke ƙaramar hukumar Chukun a jihar.

Kazalika, harin na zuwa ne mako guda bayan sace wasu mutane, ciki har da jarirai, a asibitin masu larurar kuturta da tarin-fuka da ke Zaria.

Jihar Kaduna na fama da hare-haren ‘yan bindiga inda wani rahoto da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar ta fitar a watan Afrilu ya nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na 2021 an kashe mutum 323 tare da yin garkuwa da mutum 949 a jihar.

Gwamnatin jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai, ta sha jaddada cewa ba za ta yi sulhu da ‘yan bindigar da ke garkuwa da mutane ba, tana mai cewa babban burinta shi ne ta kawar da su.