‘Yan bindiga sun sace shugaban kwaleji a Zamfara

Daga SUNUSI MUHAMMAD, a Gusau.

An sami ruɗani a Kwalejin Nazarin Harkokin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Bakura da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara a ranar Asabar yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace shugaban Kwalejin Nazarin Harkokin Gona mallakin gwamnatin jihar Zamfara, Malam Habib Mainasara a cikin gidansa da ke makarantar.

Da yake yi wa wakilinmu ƙarin haske ta waya, mataimakin rajistara na kwalejin, Malam Aliyu Atiku Bakura, ya ce ‘yan bindigar sun yi wa gidan shugaban makarantar ƙawanya ne da misalin ƙarfe 2:30 na tsakar daren Lahadi, inda suka ƙwace duka wayoyinsa da na matansa haɗa da wasu kayayyaki masu daraja da dai sauran aika-aika.

‘Yan bindigar sun tafi da Mainasara ne tare da wani mai suna Malam Kabiru Muhammed wanda malami ne a Kwalejin Kimiyya ta Bakura.

A Afrilun da ya gabata ne Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya naɗa Malam Habib Mainasara a matsayin shugaban Kwalejin Aikin Gona ta Jihar.

Ya zuwa haɗa wannan labari, wani ƙanin Mainasara, Malam Mainasara Nasiru, ya shaida wa Manhaja cewa ba su ji daga waɗanda suka sace ɗan’uwan nasu ba.

Ya bayyana cewa sun kai rahoton lamarin ga rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara da kuma DSS don kai musu ɗauki cikin gaggawa, tare da yin kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da jami’an tsaron jihar da su yi abin da ya kamata wajen tabbatar da kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa ba tare da wata illa ba.

A nasa ɓangaren, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni aka tura rundunar ceto ta musamman zuwa yankin don tabbatar da ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su lafiya.