Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex ya rasu

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna

Allah Ya yi wa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Yusuf Barnabas Bala, da aka fi sani da Bantex, rasuwa.

Bayanan na Manhaja ta kalato sun nuna Bantex ya rasu ne da safiyar Lahadi.

Marigayin ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan jihar ne a 2015 da 2019, yayin wa’adin farko na Gwamna Nasir El-Rufai.

A 2019 ne Bantex ya saki muƙamin nasa a matsayin mataimakin gwamna don neman kujerar sanata a shiyyar Kaduna ta Kudu inda abokin takararsa na PDP, Danjuma La’ah, ya kada shi.

Gwamna El-Rufai ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin rasuwar abokinsa kuma ɗan’uwa, wato Mai Girma Barnabas Yusuf Bala (Bantex)

A halin rayuwarsa, Bantex ya taɓa riƙe muƙamin shugaban Ƙaramar Hukumar Kaura, haka ma tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *