Talata, 20 ga Yuli ce Babbar Sallah – Sultan

Daga WAKILINMU

Biyo bayan bayyana Lahadi, 11 ga Yuli a matsayin 1 ga watan Zul-Hijja 1442AH da Mai Martaba Sultan na Sakkwato kuma Shugaban Majalisar Ƙoli na Harkokin Musulunci na Nijeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi, ya tabbata cewa Talata, 20 ga Yuli ita ce ranar da Musulmin Nijeriya za su yi Babbar Sallah ta bana.

Sultan ya bayyana sabon watan ne cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun Shugaban Kwamitin Bai wa Majalisar Sultan Shawara kan Sha’anin Addini, Farfesa Sambo Junaidu, a Lahadin da ta gabata a Sakkwato.

Sanarwa ta nuna cewa, “Kwamitin bai wa Majalisar Sultan Shawara kan Harkokin Addini tare da haɗin gwiwar Kwamitin Neman Wata, sun karɓi rahoto ran Asabar dangane da ganin jinjirin watan Zul-Hijja, 1442AH.

“Sultan ya yi na’am da rahoton tare da bayyana Lahadi, 11 ga Yuli a matsayin 1 ga watan Zul-Hijja Dhul-Hijja 1442AH.

“Ya yi taya murna ga Musulumin Nijeriya tare da yi musu fatan shiriyar Allah da rahmarSa.”

Farfesa Junaidu ya ce Sultan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da addu’ar fatan zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a wannan ƙasa kana ya yi fatan a yi bikin Babbar Sallah lami lafiya.