An yi kira ga gwamnatin Katsina ta riƙa tantance malamai masu koyar da maniyyata

Spread the love


Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin da ya lura da aikin Hajji da ya gabata(Amirul Hajj),Alhaji Tukur Ahmed Jiƙamshi ya yi wannan kira lokacin
da yake gabatar ma gwamna Dikko Raɗɗa rahoton kwamitin kan aikin Hajji na 2024.

Ya ce domin kaucewa matsalolin a nan gaba, ya kamata gwamnatin ta lura da malaman da take turawa domin taimakawa alhazzai wajan gabatar da ibadar su.

A cewar shugaban kwamitin,mafi yawan malaman da ake turawa musamman na ƙananan hukumomi su kansu basu san aikin ba.

Ya kuma shawarar ci gwamnati da ta ƙara sa ido wajan tantance maniyata saboda akan sami yan wasu jihohi harda da na ƙasar waje.

Haka kuma rahoton ya roƙi gwamnatin Katsina da ta ƙarfafa wa masu yaɗa labarai akan yadda aikin hajji ke gudana a ƙasa mai tsarki .

Alhaji Tukur Jiƙamshi wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar ne ya yabawa Dikko Raɗɗa a ƙoƙarin da yayi wajen samar da ingantaccen masauki kusa da ka’aba .

Haka kuma gwamnan ya biya wa Alhazzai hadaya tare da basu goron sallah a lokacin da suke tsananin buƙata.

A jawabin sa bayan da ya amshi rahoton gwamna Raɗɗa yayi alƙawarin sake duba rahoton tare da amincewa nan take da wasu roƙo da kwamitin yayi kan tantance malamai.

Ya kuma yi alƙawarin ƙarfafa wa masu kawo rahoto da kuma yaɗa labarai domin kaucewa matsalar rashin sanin halin da mahajjata ke ciki.

By ukarofi