Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar haɗin kan Funtua ta bi sahun masu kiraye kiraye ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da bada umurnin Kafa sansanin sojoji a ƙananan hukumomin da ba a kafa a kudancin jihar.
Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan kira a hira da yayi da manema labarai a garin Katsina.
Ya bayyana takaicin da sai da dai-dai lokacin da ana gab da fara girbin amfanin gona a yankin ‘yan ta’adda ke cigaba da hare hare a yankin.
Kwamred Suleiman wanda yake magana cikin damuwa da ɗimauta ya bayyana cewa gaba ɗaya kudancin jihar Katsina na cikin tashin hankali da basu taɓa gani ba .
“Manoma sun ƙauracewa gonakin su, harkokin kasuwanci ya kusa tsayawa cik ga mutane na barin ƙauyukan su sakamakon hare haren ƴan bindiga a yankin,”inji shugaban ƙungiyar.
Ya zama wajibi shugaban ƙasa cikin gaggawa ya bada umurnin Kafa sansanin sojoji da sauran jami’an tsaro da basu umurni da wa’adi na kakkaɓe waɗannan ƴan ta’adda.
Kwamred Suleiman ya yabawa muƙaddashin gwamnan jihar bisa ganawa da babban Hafsan sojojin Nijeriya da kuma kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu na ɗaukan matakin gaggawa kan taɓarɓarewar tsaro a jihar.
Sai yayi kira ga gwamnatin Katsina da ta ƙara ɗaukar jami’an tsaro na al’umma (CWC) da basu isasshen horo na sabbin dabarun yaƙi da ta’addanci domin su taimakawa sauran jami’an tsaro wajan yaƙar ta’addanci a jihar.
Haka kuma shugaban ƙungiyar tayi kira ga al’ummar jihar da su tashi tsaye wajen addu’oi na samun zaman lafiya a jihar.
Ya miƙa ta’aziya a madadin ƙungiyar ga al’ummar unguwar Mantau bisa rasa rayukan mutane 32 da ƴan bindiga suka kashe a yayin da suke gudanar da sallar Asuba a masallaci.
