Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Uwargidan Gwamnan Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Raɗɗa ta yi kiran a wajan taron ranar Cutar polio a Katsina.
Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnatin jihar Katsina ya sami halartar ƙungiyoyi da dama da suka haɗa da ƙungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO da ƙungiya da ke kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF da wasu ƙungiyoyi na ƙasa masu zaman kansu.
Akwai wakilan malaman addini da na sarakunan gargajiya da matan shugabannin ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jihar.
Uwargidan Gwamnan ta ce babu shakka akwai rawar da matan shugabannin ƙananan hukumomi za su taka wajen faɗakar da iyaye mata mahimmancin allurar riga-kafin shan inna da sa ran an fara gudanar da allurar a yankunan su.
Hajiya Zulaihat ta nuna jin daɗin ta ganin yadda aka sami cigaba wajen yaƙar cutar da a halin yanzu ya kusa zama tarihi.
Ta bayyana cewa a shekarar 2012 aka sami ɓullar cutar har guda 17 a ƙaramar hukumar Batsari wanda tun a lokacin ba a sake samun ɓullar cutar ba sai a wannan shekara yara da suka kamu guda biyu a ƙaramar hukumar Ɗanmusa.
Ta yi godiya ga ƙungiyoyin sa kai kaman su UNICEF da ROTARY CLUB da malamai da kuma sarakuna gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki ga irin taimako da haɗin kai da suke ba gwamnati wajen faɗakarwa da tare da yaƙi da kamuwa da cutar shan inna da sauran cututtuka a jihar.
Wakilan kula da lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya WHO Dr Jamilu Runka ya jaddada ƙudirin WHO na tabbatar da duk wani yaro jariri har zuwa watanni 59 anyi masa allurar riga-kafi da cutar ƙyanda a jihar.
Ita ma wakiliyar UNICEF Fatima Adamu ta taya uwargidan Gwamnan Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Raɗɗa bisa shirya wannan taro da ta ce ba ranar biki ba ne sai da a cigaba da aiki tuƙuru wajen kawar da wannan cuta.
Sauran waɗanda suka yi magana sun haɗa da wakilan malaman addini, sarakunan gargajiya da matan shugabannin ƙananan a jihar.
Taron ya sami halartar yara da manya masu nakasa sakamakon kamuwa da cutar shan inna a jihar.
