Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Shugaban ƙaramar hukumar Balanga a Jihar Gombe, Ibrahim Salisu Jatau ya buƙaci iyaye da masu kula da yara da su fito da ’ya’yansu domin yin rigakafin cutar shan inna, yana mai tabbatar da cewa rigakafin ba ta da wata illa ga lafiyar yara.
Jatau ya yi wannan kira ne yayin ƙaddamar da bikin ranar yaƙi da cutar shan inna ta duniya ta shekarar 2025, wanda ƙungiyar Rotary ta shirya domin inganta lafiyar yara a faɗin Jihar Gombe.
A cewarsa, “Allurar rigakafin shan inna tana da matuƙar muhimmanci, kuma babu wata illa a cikinta. Abin da ake buƙata kawai shi ne ƙarin wayar da kai domin mu tabbatar cewa dukkan yaranmu sun samu kariya daga wannan cuta.”
Ya ce gwamnati na aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya wajen yaɗa wannan saƙo domin kowane gida ya fahimci muhimmancin rigakafi.
A nasa jawabin, jami’in International Vaccine Access Centre (IVAC), Adamu Babayo, ya bayyana cewa ƙaramar hukumar Balanga na da al’umma kimanin mutane 400,000 inda aka tsara yi wa yara 8,346 rigakafin shan inna a mazaɓu 10.
Babayo ya ce an samar da allurai isassu da za su wadatar da dukkan yara da ake niyya, tare da kira ga iyaye da su tabbatar sun kai ’ya’yansu wajen rigakafi don kare su daga cutar.
Haka kuma, shugaban cibiyar kula da lafiya ta SWA PHC, Mista Danjuma K. Mauni, ya bayyana cewa rigakafin shan inna na taka muhimmiyar rawa wajen kare lafiyar yara, inda ya yaba wa ƙungiyar Rotary bisa haɗin gwiwar da take yi da gwamnati wajen gudanar da wannan rana ta musamman.
A ƙarshen taron, Ibrahim Salisu Jatau ya jagoranci ƙaddamar da yaƙin rigakafin ta hanyar ɗigawa wasu ƙananan yara allurar, a matsayin alamar fara bikin ranar yaƙi da cutar shan inna ta duniya, wacce ake gudanarwa duk shekara a ranar 24 ga Oktoba.
Jatau ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar Balanga za ta ci gaba da tallafawa shirye-shiryen lafiya da suka shafi kariyar yara domin tabbatar da cewa babu yaro da zai rasa rigakafin a yankin.
