Borno: An datse hannun manomi a harin makiyaya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin makiyaya ne Jihar Borno suka farmaki wani manomi mai suna Mohammed Ali Fantami a Ƙauyen Jakana da ke Ƙaramar Hukumar Konduga.

A cewar mai sharhi akan harkokin tsaro, Zagazola Makama al’amarin ya auki ne a ranar Laraba a lokacin da wasu makiyaya suka bar dabbobinsu suka yi kutse acikin wata gonar wake na mazauna yankin inda suka lalata amfaninta.

A yayin da wani manomi ɗan shekara 30 ya yi yunƙurin korar dabbobin, sai ɗaya daga cikin makiyayan ya kai masa hari da makamin da ke hannunsa, inda daga bisani suka datse masa hannu da yi masa mummunan rauni a wuya kafin suka tsere.

Tuni aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Maiduguri (UMTH), inda a nan ake masa magani.

A ƴan shekarun nan manoma na fuskantar hare-haren makiyaya a sassan Nijeriya, lamarin da yasa Marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya samar da shirin ware yankin kiwo a karkara domin kawo ƙarshen faɗace-faɗace a tsakanin ɓangarorin biyu.

Saidai hakan bai samu karɓuwa ba musamman a yankin kudancin Nijeriya domin kuwa har yanzu ana takusa saƙa a tsakanin ɓangarorin.

By Babaji