Gwamnatin Kano ta ɗage aikin tsaftar muhallin ƙarshen wata

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ɗage aikin tsaftar muhalli na ƙarshen watan Oktoba 2025 da aka tsara gudanarwa a gobe Asabar.

Wannan mataki ya biyo bayan shirye-shiryen babban bikin baje kolin gargajiya da gwamnatin jihar ta shirya, wanda ya zo daidai da ranar da ake gudanar da tsaftar muhalli.

A cewar sanarwar da sashen wayar da kai na ma’aikatar muhalli ta jihar ya fitar a ranar Juma’a, 25 ga Oktoba 2025, ta ce an ɗage aikin ne domin bai wa jama’a damar halartar taron baje kolin cikin natsuwa da tsari.

Sai dai ma’aikatar ta shawarci al’umma da su ci gaba da tsaftace muhallansu, duk da ɗage aikin, domin kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga kowa da kowa.

By ukarofi