An yi sallar jana’izar da babu gawa kan mahaifin Kakakin Majalisar Dokokin Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Ɗaruruwan Musulmi ne suka hallara a gidan Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Nasiru Mu’azu Magarya a Gusau a jiya Litinin, inda aka gudanar da sallar jana’iza ga mahaifinsa wanda ya mutu a hannun ‘yan ta’adda bayan sun yi garkuwa da shi da matarsa da jaririyart ‘yar sati uku da wasu ‘yan’uwansa su uku makonni takwas da suka gabata.

Sheik Abubakar Fari wanda shi ne shugaban tuntuɓa na malaman jihar, shi ne ya jagoranci Sallar jana’izar tare da shugaban majalisar jihar, haɗa da fitattun malaman addinin Musulunci, da manyan jami’an gwamnati da ɗaruruwan Musulmai daga ciki da wajen jihar.

A hirar da ya yi da MANHAJA jim kaɗan bayan sallar jana’izar, Sheik Tukur Sani Jangebe wanda shi ne tsohon kwamishinan lamurran addini kuma limamin masallacin Juma’a na Muslims foundation a Gusau a halin yanzu, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

A cewarsa, sallar jana’izar da babu gawa a gaban liman an samo ta ne daga Annabi Muhammad (SAW) inda ya umarci Musulmai su riƙa aiwatar da ita idan an kasa samar da da gawar mamaci.

“Yana cikin hadisin Annabinmu mai daraja Muhammadu (SAW) yin irin wannan sallar jana’izar ga mamacin da ya mutu amma aka kasa gano gawarsa”, cewar Sheik Jangebe.

Sheik Jangebe yayi kira ga Musulmai da su ci gaba da yin addu’a cikin haƙuri don Allah Maɗaukakin Sarki Ya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da ke addabar yankin arewacin ƙasar nan da ma Najeriya baki ɗaya.

Idan za a iya tunawa, Jaridar Blueprint ta ruwaito a ranar Asabar cewa mahaifin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Hon. Nasiru Muazu Magarya, mai suna Alhaji Mu’azu Abubakar Magarya wanda aka yi garkuwa da shi makonni takwas da suka gabata tare da matarsa da jaririya ‘yar makonni uku haihuwa da wasu mutane uku, an ce ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane sakamakon bugun zuciya.

Yayin da ake gabatar da sallar janazar

Babban ɗan’uwan mahaifin kakakin majalisar da aka sani da Malam Ɗahiru Saraki Magarya a wata hira da Blueprint jim kaɗan bayan kuɓutar da su ba tare da wani sharaɗi ba da ‘yan sanda tare da had’ɗin gwiwar sojoji a hedikwatar rundunar da ke Gusau ranar Asabar.

Malam D’Ɗahiru Saraki Magarya ya ce ɗaya daga cikin ‘yan bindigar sarkin da aka fi sani da Kachalla ne ya sanar da shi kwana guda kafin jami’an tsaro su ceto su cewa ɗan’uwansa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya yayin da yake hannun ‘yan bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *