Ana wata ga wata…

Daga IBRAHIM YAYA

A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda hukumomi da masana a fannin yaƙi da sauyin yanayi, na yin gargaɗi game da yadda yunwa za ta addabi sassan duniya. Wai ana maganar “targaɗe sai ga karaya”. Masana sun sha yin kashedi tun kafin annobar cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba ganin irinta ba, tun a lokacin yaƙin duniya na biyu, saboda wasu dalilai.

Amma duk da wannan babbar matsala da aka yi hasashen za ta kunno kai, masana sun sha faɗawa zaman muhawarar kwamitin sulhun MDD a lokuta daban-daban kan yadda za a kare fararen hula da yunwa ta shafa sakamakon rikici cewa, yayin da ake fama da COVID-19, ba kawai muna fama da annobar lafiya da ta shafi duniya baki ɗaya ba, har ma ta haifar matsalar jin kai.”

Wasu alƙaluman da aka fitar game da matsalar abinci da duniya ke fuskanta, na nuna cewa, kimanin sama da mutane miliyan 800 ne suke kwana da yunwa a duniya. Akwai kuma ƙarin sama da mutane miliyan 100 dake fama da matsalar yanayi na yunwa ko fiye da haka.

Wannan ya sa kwararru, yayin taron ƙaddamar da rahoto na 6 na sassan gwamnatocin nahiyar da ya gudana a Nairobin Kenya game da sauyin yanayi ko IPCC a taƙaice, taron da ya gudana a gefen ci gaban taron dandali na 5, na hukumar MDD mai lura da muhalli ko UNEA-5, buƙatar samar da isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukan daƙile tasirin sauyin yanayi tun daga tushe, domin bai wa nahiyar damar jurewa alamun sauyin yanayi kamar fari, da ƙaruwar zafi, da wutar daji, tare da yaɗuwar cututtukar da wasu halittu ke bazawa.

Ƙwararrun na ganin cewa, cimma nasarar kafa tsarin da zai bai wa nahiyar Afirka damar jure mummunan tasirin sauyin yanayi, da muhalli mai inganci, ya dogara ne ga nasarar samar da isassun kuɗaɗen gudanar da muhimman ayyuka masu nasaba da hakan.

Baya ga matsaloli na rashin abinci sakamakon matsalar sauyin yanayi, hukumomin kuɗi irinsu Bankin Duniya ya yi hasashen cewa, za a samu raguwar kuɗaɗe a ƙasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara, sakamakon matsalar tattalin arziki da cutar COVID-19 ta haifar gami da rufe wuraren ayyukan yi.

Sai dai, duk da hasashen da bankin ya yi na kaso 4 cikin 100 na al’amura za su farfaɗo a shekarar 2021 da ta gabata, a hannu guda kuma, al’amura za su sake komawa baya, saboda raguwar kuɗaɗen shiga da ayyukan yi da ma’aikata ‘yan ci-rani za su fuskanta, matakin da zai ƙara haifar da rasa ayyukan yi da kudin shiga sakamakon matsalar tattalin arziki a ƙasashen da suke zama.

Yayin da duniya ke ƙara koyon darussa da dama daga COVID-19, da sauran bala’u daga indallahi, haƙiƙa lokaci ya yi da za a karkata ga tunanin shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, wato gina kyakkyawar makoma ta bai ɗaya ga ɗaukacin bil-Adama, don samun duniyar da kowa zai ji dadin zama a cikinta cikin kwanciyar hankali da walwala.