Za mu soma fitar da fetur ba dare ba rana – NNPC

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya ce babu buƙatar ‘yan Nijeriya su riƙa sayen fetur suna ɓoyewa saboda a cewarsa an tanadi wadataccen mai da za a fitar.

Shugaban NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya Laraba a Abuja jim kaɗan bayan ganawarsa da ƙungiyar ma’aikatan man fetur da ƙungiyar direbobi masu jigilar mai (PTD) da ƙungiyar ‘yan kasuwar mai (DAPMAN) da kuma ƙungiyar manyan ‘yan kasuwar mai (MOMAN).

Kyari ya ce, “ba a fama da ƙarancin mai a ƙasar nan, jerin gwanon abubuwan hawa da ake gani a gidajen mai wahala ce kawai. Mutane su sayi daidai abin da suke buƙata.

“Muna tabbatar muku da cewa muna da isasshen man fetur da kowa zai samu, amma muna bada haƙuri bisa wahalar da mutane ke sha.”

Ya ƙara da cewa, Nijeriya na da isasshen man da za ta fitar da mai daga masuakin mai don taƙaita wahalar da ake sha a kansa.

“Kawo yanzu akwai litar mai bilyan 1.7 a hannunmu, hakan na nufin cewa muna da zarafin fitar da mai daga defot ɗinmu duka.

“Mun shirya yadda za a fitar da mai daga defot ba dare, ba rana.

“Wannan zai taimaka wajen hana ajiyar man da sayan man da mutum bai buƙata, kamar yadda muke gani a gidajen mai yau. Abubuwa za su dawo daidai,” in ji Kyari.