Kwankwaso ya tattara komatsansa don ficewa daga PDP

Daga WAKILINMU

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa kafin ƙarshen watan Maris da ake ciki zai sauya sheƙa ya fice daga jam’iyyar PDP.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa kamar yadda kafar ta bayyana.

Kwankwaso ya tabbatar da cewa ya yi nisa da shirinsa na neman sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP.

Wata majiya ta kusa da jigon siyasar ta bayyana cewa, rashin tsari dangane da yadda ake tafiyar da sha’anin jam’iyyar PDP shi ne babban dalilin da ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara komatsansa don ficewa daga cikinta.

Idan ya tabbata Kwanso ya bar PDP, wannan shi ne zai zama karo na uku da ɗan siyasar zai sauya sheƙa daga 2014 zuwa yau.

Don kuwa, a 2014 Kwankwaso ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, a 2019 ya sake sauya sheƙa zuwa PDP daga APC, sai kuma a wannan karon da yake shirin barin PDP zuwa wata sabuwar jam’iyya.