Soyayya ce sanadiyyar fara rubutuna- MD Asnanic

“Marubuci mutum ne mai keɓaɓɓiyar ƙwaƙwalwa”

Daga AISHA ASA

Sanannen abu ne, Arewacin Nijeriya kewaye ta ke da albarkatun ƙasa da ko su kaɗai mu ka doga da su, za su iya cin ƙarfin buƙatunmu. Duk da wannan ni’ima da aka ba mu, Allah ya mana daɗɗi da baiwar ƙirƙira, musamman a tsakanin matasanmu. Muhammad Iliyass, wanda aka fi sani da MD Asnanic, matashi ne da ƙwaƙwalwarsa ke zagaya tsakanin ɓangarorin rubutu, kai har ma da na rera waƙa. A taƙaice, matashi ne mai ƙwaƙwalwar mutane da yawa. A wannan makon, shafin adabi na jaridarku mai farin jini, Manhaja, ta samu damar tattauna wa da matashin. Mai karatu, idan ka shirya, Aisha Asas ce tare da MD Asnanic:

MANHAJA: Sunanka sananne ne a duniyar rubutu, don haka tarihinka ne buƙatar masu karatunmu.
MD ASNANIC: Sunana MD Asnanic. A asibahin wata Juma’a, 14 ga watan Fabrairu, 1992, Allah ya ƙaddara haihuwata a gida mai lamba 75 Kwanar Chanchangi Tudun Wada Kaduna.

Na yi ‘primary’ da ‘secondary’ dukka a garin Kaduna, na yi ‘ibtida’iyya’ tare da sauke Alƙur’ani mai girma, sannan na tafi ‘sanawiyya’ dukka dai a garin Kaduna. Bayan nan na tafi ‘National Open University’ yayin da na yi ‘B.A Islamic Studies’. A yanzu kuma ina karatun ‘B.A Hausa and Linguistics’ a Kaduna ‘State University’. Har yanzu ina ci gaba da ɗaukar karatun addini a gaban malamaina na zaure. Duk wani abu da ya shafi al’adar Hausa shi ya fi burge ni; tun daga kan abinci da sutura da sauransu.

Mutane masu kawaici da haƙuri suna burge ni, da su na fi son yin mu’amala, haka zalika masu zumunci. A cikin launuka kuma na fi son koren launi (green colour), yanayin shekara kuwa na fi son damina. Wannan shi ne MD Asnanic a taƙaice.

A wacce shekara ka fara rubutu?
Na fara rubutu a shekarar 2007, lokacin ina ɗan aji uku a ‘secondary school’.

Za mu so ka kaimu lokacin da ka fara ɗora alƙalami da zumar fara rubuta littafi.
Idan zan ɗauki masu karatu, in cilla su zamanin da na fara ɗora alƙalamina kan takarda sai dai in fara da musabbabin da ya sa ni rubutu, wanda ba komai ba ne face soyayya. Tun ina da ƙuruciya, na yi wata soyayya da ba zan manta da ita ba, don haka sai na rubuta ɗan ƙaramin kudin tarihin wannan soyayya, wanda a taƙaice zan iya kira ‘diary’. Bayan shi sai na rubuta littafina na biyu kuma na farkon shiga kasuwa.

Marubuta mata ne suka fi samun wurin zama a duniyar adabin kasuwar Kano. Ko hakan ya sa ka fuskanci wani ƙalubale yayin gabatar da litattafanka?
Eh to, ba zan ce ban fuskanci ƙalubale ba, amma kuma ƙalubalen da na fuskanta ba shine damuwata ba, domin a lokacin ban sa rai da samun kuɗi ba, yayin da na ba ‘yan kasuwa litattafan, ni dai burina rubutana ya fita, a dinga ƙirga ni a sahun marubuta.

Marubuta litattafan Hausa musamman na Arewa, ba sa samun tagomashi da kuma alfano da marubuta na wasu ɓangarori ke samu, duk da cewa, Hausa ta kasance zuciyar Afrika. Ko me ya sa?
Dalili ɗaya ne, rashin ɗaukar abin da muhimmanci. Kuma hakan ya samo asali ne ta dalilin ƙarancin neman ilimi da al’ummarmu ta tsinci kanta a ciki, wanda ke da ilimi shi yake iya karanta wa idan an rubuta, ku ma shi ke daraja rubutu.

Kafin mu yi nisa, shin wane ne za a iya kira marubuci?
Ma’ana ta zahiri:-Marubuci na nufin duk wani mutum da ke da ikon ɗora alƙalami a kan takarda ko ma’ura ya rubuta wasu haruffa a matsayin magana, kuma a iya karanta wa su bayar da ma’ana.


Ma’ana ta Ilimi:- Marubuci wani mutum ne mai wata irin keɓaɓɓiyar ƙwaƙwala ta musamman da yake iya amfani da ita wajen tasarifin abubuwan da ke faruwa kewaye da shi, ya mayar da su ƙirƙirarriyar wallafa (Zube, waƙa ko wasan kwaikwayo), cikin salo mai armashi da fasahar harshe.

Me ya bambanta marubuta da ke buga litattafansu da kuma masu rubutu a yanar gizo, wato ‘online writers’?
Kai tsaye zan iya cewa tasiri ne na zamani da kuma rashin samun damar bugawar. Dalilin da ya sa na ce haka shi ne, rubutun ‘online’ ya samo asali ne daga rashin samun damar buga littafi a sayar wa da ‘yan kasuwa, saboda kyauta ake saka shi a yanar gizo a farkon lokaci. Amma a yanzu ya zama wani abu da zamani ya yi kaka-gida a cikinsa, hatta masu bugawar su ma sukan sayar da littafi ‘online’ saboda tasirin zamani.

Zuwan ‘online writers’ ci gaba ne a adabin Hausa ko ci baya?
Gaskiya ci gaba ne sosai a tawa fahimtar. Domin ta wannan hanyar rubutun Hausa ya zagaye duniya a cikin ‘internet’ fiye da yadda ake tunani. Sannan abu ne mai tafiya da salo irin na zamani.

Shin da gaske marubuta a yanar gizo ne suka kashe kasuwar littafai?
Ba zan dora musu laifi kai tsaye ba, amma wayoyin sadarwa na zamani suna daga cikin abin da suka taimaka wajen durƙushewar kasuwar bugaggun littattafai. Amma babban abin da ya fi bayar da gudunmawa wajen rushewar kasuwar bugagen littafi su ne ‘yan kasuwar littafi, mafi yawancinsu ba su da amana.

Littafai nawa ka wallafa?
Na rubuta littattafai a ƙalla 22 a yanzu, amma guda ɗaya ne ya shiga kasuwa, biyu kuma na sake su a yanar gizo.

Baya ga rubutu na zube, ko kana da wata baiwa ta ƙirƙira?
Nakan yi rubutun fim, wanda masana sun tabbatar wasan kwaikwayo ne. Haka zalika ni mawaƙi ne, hasali ma waƙar ita na fara yi kafin rubutun zube da na Fim.

A wane lokaci ka fi sha’awar rubutu?
Duk lokacin da na ke cikin farin ciki na fi jin daɗin rubutu ko waƙa. Musamman a yanayin sanyi na hunturu ko sanyin damina.

Ya kake samun jigo idan za ka yi rubutu?
Mafi yawanci jigon labaraina daga wani fanni na ilimi na ke naƙalto su, ko abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Idan na ce fannin ilimi; misali in ji wani likita ya yi bayanin wayar da kai game da wata cuta, to ni kuma dai in ƙirƙiri labari a kan haka. Ko kuma in ga wata al’ada da ke neman danne addini da makamantan haka.

Ta ya marubuta za su iya zamanantar da rubutunsu?
Ta hanyar rubuta abin da zai dace da tunani, da amfani da ilimi ta fusakar binciken abin da ake rubutu a kai, da kuma binciken inda duniyar rubutu ta sa gaba a duniya.

A marubuta kana da gwani?
Tabbas ina da shi. A marubutan da suka shuɗe, Abubakar Imam ne gwanina. A cikin marubutanmu na zamani Nazir Adam Salih. A cikin marubuta mata kuma Maimuna Idris Beli da Aisha Asas.

Ko akwai wani abu da ba za ka manta da shi ba a alaƙarka da rubutu?
Sanadiyyar rubutu na haɗu da mutanen da ko a mafarki ban yi tsammanin haɗuwa da su ba, ba zan taɓa manta wannan ba. Kuma na samu lambar yabo a sanadiyyar rubutu.

Wacce nasara ka samu a harkar rubutu?
Nasara da na samu a rubutu ita ce, shahara da kuma karɓuwar rubutuna a wurin mutane. Alhmdu lillah!

Wane kira za ka yi ga marubuta masu tasowa?
Kada su sa a ransu za su yi rubutu don kud’ɗi ko tara abin duniya; su yi shi a matsayin abin da ransu ke so kuma su suka sa kansu sannan su tsarkake niyya.

Wacce shawara za ka ba wa marubuta littafai a wannan lokaci da kasuwarsu ta kwanta?
Marubutan da kasuwarsu ta kwanta ina ba su shawara da su bi zamani, domin ta inda ƙwarya ta fi karkata ta nan ruwa ke zuba. Allah ya sa mu dace.

Amin. Mun gode
Ni ma na gode ƙwarai.