Sau 11 aka gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu a Sin

CRI HAUSA

Yau Alhamis, ofishin yaɗa labarai na gwamnatin ƙasar Sin, ya fidda takardar “raya harkokin motsa jiki ta nakasassu da kare ikonsu”. Cikin takardar, an ce, ’yan wasan motsa jiki 96, za su halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta nakasassu a lokacin hunturu da za a buɗe a birnin Beijing.

Cikin takardar, an ce ƙasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa ga bunƙasar harkokin motsa jiki na nakasassu a fadin duniya. Daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2020, tawagar ’yan wasan motsa jiki ta nakasassu ta ƙasar Sin, ta halarci gasannin ƙasashen duniya guda 160, inda suka lashe lambobin yabo na zinari guda 1,114. Kuma, tun daga shekarar 1984 da aka fara gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu a ƙasar Sin, ya zuwa yanzu, gaba ɗaya an gudanar da gasanni sau 11 a cikin ƙasar.

Haka kuma, kakakin ƙungiyar hadin gwiwar nakasassu ta ƙasar Sin Guo Liqun ya bayyana cewa, gwamnatin ƙasar Sin tana mai da matuƙar hankali wajen kare ikon nakasassu, da samar da wani yanayi na kawar da duk matsaloli ga nakasassu, da kuma ba da tallafi gare su.

Fassarawa: Maryam Yang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *