Duk mace mai aiki tsakanin maza tana tare da ƙalubale – Laraba Ahmed

“Rashin sauke haƙƙin aure ne ke sa wasu mata ɗora wa ‘ya’yansu talla”

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Hajiya Labara Ahmed Kawu, Shugabar ƙungiyar nan mai zaman kanta ta ‘Ahmed Kawu Hearth for Children Initiative’, marubuciya da ta rubuta littafin koyon Fulatanci na ‘Ekkito Fulfulde’, kuma babbar sakatariya ce a aikin gwamnati, wato ‘permanent Secretary’ da ke hukumar kula da ƙananan hukumomi da kuma sanya ido a ofishin shugaban ma’aikata na Jihar Gombe. Gogaggiyar ma’aikaciya ce, wacce yanzu haka saura mata watanni uku ta yi ritaya. A cewar ta, ba ta da burin da ya wuce ta inganta rayuwar mata da tallafa wa almajirai. A tattaunawar ta da shafin Gimbiya na jaridar Manhaja, ta bayyana irin gwagwarmayar da ta yi da kuma halin da ta ke ciki a yanzu haka da ta share shekaru 34 tana aikin gwamnati. Ta kuma bayyana wa Manhaja, ta fara aiki ne a matsayin jami’ar labarai a Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta tshohuwar Jihar Bauchi (Information Officer) har ta kai matakin mataimakiyar darakta a wannan ma’aikatar ta yaɗa labarai. Yanzu haka ita ce Babbar Sakatariya a Hukumar kula da Ƙananan Hukumomi ‘Local Government Services Commission’. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: ko wacce ce Hajiya Laraba, kuma wacce irin gwagwarmaya ta yi a rayuwa?
HAJIYA LARABA: ni dai sunana Hajiya Laraba Ahmed Kawu, an haife ni a garin Gombe, kuma Bafulatana ce gaba da baya, domin kakannina ma na uku dukkansu Fulani ne. A nan garin Gombe aka haifeni, a ranar 7, ga watan Nuwamba, shekara ta 1962, kuma a nan na yi ƙuruciyata har na kai lokacin shiga makaranta. Iyayena suka sani a makarantar firamare ta Jankai wacce yanzu ta koma Jalo Waziri Firamare, a shekara ta 1969 zuwa 1975. Bayan nan sai na samu sa’ar tafiya sakandaren gwamnati ta garin Billiri a Jihar Gombe a shekarar 1975 zuwa 1978, inda na yi aji uku, daga nan sai na sake tafiya sakandaren ‘yan mata ta Doma da ke garin Gombe a shekarar 1978 zuwa 1980. Bayan da na kammala sakandare na rubuta jarrabawar WAEC, sai na samu tafiya zuwa jami’ar Usmanu X
Ɗanfodiyo da ke garin Sakkwato, wato UDUS, a tsakanin shekarun 1980 zuwa 1985, inda na samu takardar shaidar karatu na matakin digiri na farko a ɓangaren tarihi, wato ‘B.A History’. Ina nan sai na sake tafiya jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi, ATBU, na yi babbar diploma a vangaren sha’anin mulki wato ‘PGD on Management’.

Ko Hajiya ta yi aikin gwamnati? 
Ƙwarai kuwa. Na yi aiki, ina ma kai. Na fara aiki ne a matsayin jami’ar labarai, wato ‘Information officer II’ a Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta tsohuwar Jihar Bauchi, a shekarar 1987, Ina nan ina aiki a wannan ma’aikatar har tsawon shekaru uku, a shekara ta 1990 sai na yi canjin wajen aiki, na koma Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi, a matsayin mai kula da ƙananan hukumomi ‘Inspector of Local government’, daga shekara ta 1990 har zuwa watan Yuli na shekara ta 2011, lokacin na samu ƙarin girma na zama mataimakiyar darakta. A wannan shekarar (2011) sai na koma Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe, wato SEMA (State Emergency Management Agency), inda a nan na zama Daraktar Mulki da Kuɗi (DAF) ‘Director Administration and Finance’. Ina SEMA a matsayin DAF sai na samu ƙarin girma na zama babbar sakatariya, wato ‘Permanent Secretary’, inda na yi aiki a ma’aikatu da hukumomi irin, Hukumar Kula da Ƙananan Hukumomi da Ma’aikatar Mata da walwalarsu da Ma’aikatar Lafiya da Hukumar bada Fansho ta jiha, wato ‘State Pension Board’. Daga nan sai aka mayar da ni Ma’aikatar Albarkatun ruwa. Yanzu kuma ina Hukumar kula da Ƙananan Hukumomi, Ina mai sa ido a ofishin shugaban ma’aikata na jiha, sai dai saura min watanni uku na yi ritaya daga aikin gwamnati.

Wane irin ƙalubale Hajiya ta fuskanta a wannan gwagwarmayar rayuwa ta aiki?
Ƙalubale ba za a rasa ba, domin akwai wahala wajen haɗa aikin gida da kuma na ofis, ga rubuta littafi da na ke yi a lokacin kafin na gama, domin aiki ne da na yiwa al’umma musamman al’umma ta Fulani da na bai wa gudunmawa. Na rubuta littafi akan su, domin duk macen da ta ke aiki a tsakanin mazaje, tana tare da ƙalubale, saboda yadda za ki dinga cuɗanya da waɗannan mazajen dole ne mace ta yi dukkan mai yiwuwa don ta ga ta kare kanta musammam ma mai aure, domin dole sai wani ya furta miki maganar da ba ta da daɗin ji. Sannan kuma al’umma irin ta mu Hausa Fulani, akwai matsala na ganin cewa, tunda maza aka fi sani da fita wajen aiki, ke mace duk yadda za ki yi ƙoƙari na ganin kin yi ƙwazo sai wani ya shatile mi ki ƙafafu ya nuna ya fi ki ƙwazo.

Wacce irin nasara ki ka samu?
Eh, nasara kam alhamdu lillahi, an same ta, domin albarkacin wannan aiki da na ke yi, ya rufa min asiri, inda na samu na iya tarbiyyar ‘ya’yana, kuma na ɗauki nauyin wasu ‘yan’uwa har ma na aurar da ƙannena guda bakwai. A dalilin wannan aiki na san jama’a musammam ma a aikin da na yi na bada agajin gaggawa na SEMA, inda duk inda aka samu wata annoba ina daga cikin masu shiga gida-gida muna ɗaukar bayanai na abinda ya faru, sannan gwamnati ta bada tallafi ta hannunmu, mu kuma mu raba wa jama’a. A gaskiya alhamdu lillahi.

Ko Hajiya tana cikin wasu ƙungiyoyi?
Ina da qungiya ta mata mai suna, ‘Taufiq women group’. Mu na koya wa mata sana’oi, Ina kuma da ƙungiyata mai zaman kanta ta ‘Ahmed Kawu Hearth for Children Initiative’, wadda mu ke taimaka wa yara musamman almajirai wajen koya mu su sana’oi da kula da lafiyar su, sannan mun samu haɗin kan ‘Islamic Solidarity Found’ da ke Jidda a Ƙasar Saudi-arebiya sun tallafa mana mun sayi tankin ruwa da mu ke raba wa makarantun tsangayu guda 10 ruwa, sau biyu a mako, a ranakun Litinin da Alhamis, sannan mu na sake neman masu bada tallafi domin mu faɗaɗa, amma za mu yi dukkan mai yiwuwa don ganin jama’a sun shigo sun taimaka.

Mene ne burinki a rayuwa?
Burina a rayuwa shine; idan na yi ritaya, na bar aiki, zan samu lokaci sosai da zan iya ci gaba da gudanar da ayyukan da na ke yi na jin-ƙai ta wannan ƙungiya, don kyauta ta rayuwar yara musamman almajirai da ke makarantun tsangaya da marayu ko waɗanda iyayensu ba su da ƙarfi, don dogaro da kai da sauran al’amuran rayuwa, musamman wajen ganin makarantarsu da saya mu su magani da kuma yadda za su dinga tsabtace jikinsu, kuma za mu iya yi mu su aure idan suka girma.

Ko Hajiya ta taɓa zuwa wasu ƙasashe?
Eh, ƙwarai; na je Saudi Arebiya, na je Ruwanda.

To, bari mu koma ɓangaren iyali.
Alhamdu lillahi. Allah ya albarkace ni da ‘ya’ya guda uku. Maza biyu, mace ɗaya. Ina da kuma jikoki bakwai, kuma dukkansu sunyi karatu. Babban ya gama karatunsa, yanzu Dakta ne mai digiri uku. Ita kuwa ta biyu ita ma ta kammala karatun ta na jami’a. Ƙaramin ma yana jami’a.

Wacce shawara za ki bai wa iyaye?
A kullum shawarar dai ita ce; Ina mai kira da babbar murya ga iyaye da su sa ‘ya’yansu mata a makarantar boko, don su samu ilimin zamani, ilimin addini kan wannan dole ne. Ilimin zamanin nan zai taimake su wajen sanin ‘yancinsu da kuma iya tarbiyyantar da na su ‘yaýan kamar yadda ya dace. Rashin ilimi ga ‘ya mace akwai ciwo, domin ko zaman gidan miji ba za ta iya shi yadda maigidan ta zai ji daɗin zama da ita ba, kuma koda ba za ta yi aikin gwamnati ba bayan ta yi karatun, ai ilimin zai taimake ta wajen tafiyar da sana’oi irin na cikin gida cikin sauƙi. Kuma Ina ƙara yin kira da babbar murya har ila yau, iyaye da su guji ɗora wa ‘ya’yansu mata talla, domin ita talla na haifar da lalacewar tarbiyyarsu, duk da ma dai ba kowacce uwa ce ta ke son ɗora wa ‘yarta talla ba, sai ya zama dole. A lokacin da magidanta suka kasa sauke nauyin da ke kan su wajen gudanar da ɗawainiyar gidajensu kamar yadda shari’a ta ɗora mu su, duk da cewa, malamai suna jan kunnen magidanta cewa, su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da ke kan su, domin ba haƙƙin mace ce ciyar da gida ba, amma kai namiji ka ƙasa, ka bar matarka da nauyi. Wannan ba adalci ba ne.

Hajiya mu na godiya.
Ni ma na gode kwarai.