Gasar Paralympic ta 2021 za ta ingiza aikin raya sha’nin wasan motsa jiki na nakasassu na duniya

Daga AMINA XU

An rufe gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing kwanan baya, nan da nan ne an canja na’urorin ƙauyukan Olympics dake Beijing, da garin Yan Qing da birnin Zhang Jiakou dake lardin Hebei, don dacewa da gasar Paralympic wato gasar Olympics ta nakasassu, haka nan an shirya tsaf don gudanar da gasar dake tafe.

An kammala gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing lami lafiya duk da cewa cutar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a duniya. Hakan ya ƙara wa al’ummar duniya ƙwarin gwiwar cimma nasarar gudanar da gasa ta nasasassu da za a buɗe a ranar 4 ga watan da muke ciki, matakin da zai ingiza aikin raya sha’anin wasan motsa jiki na nakasassu na duniya musamman ma a fannin gasanni a lokacin hunturu.

‘Yan wasanni na nakasassu na tinkarar mawuyacin hali, suna kokari yin takara gwargwadon ƙarfinsu, suna alfahari kuma sun cancanci yabo. Gasar Olympic da ajin nakasassu na gasar suna da ban sha’awa gaba ɗaya. Shuey Rhon Rhon na shiryawa tsaf, bari mu zura ido ga gasar.

Mai zane: Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *