Mike Pompeo ya ziyarci Taiwan ne da mugun nufi

Daga CRI HAUSA

Yau ne, tsohon sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Mike Pompeo ya ziyarci yankin Taiwan na ƙasar Sin tare da mugun nufinsa, wanda kullum yake yunƙurin zama shugaban Amurka. Nufin Mike Pompeo na ziyartar Taiwan a wannan karo, shi ne domin neman samun goyon bayan masu adawa da ƙasar Sin a Amurka da kuma ƙarfafa tasirinsa.

Kwana guda kafin Mike Pompeo ya ziyarci Taiwan, gwamnatin Amurka ta aika da wata tawaga mai ƙunshe da tsoffin jami’an tsaron ƙasa zuwa Taiwan, lamarin da ya nuna cewa, dukkan jam’iyyun siyasar Amurka waɗanda suka yi mulki ko ba su yi mulki a ƙasar ba, sun mayar da Taiwan a matsayin wani wuri da zai ba su ribar siyasa da kuma samun ƙuri’u.

Sanin kowa ne cewa, ƙasar Sin ɗaya ce tak a duniya. Ba wanda zai iya raba Taiwan daga ƙasar Sin. Dole a dinki ƙasar Sin baki daya, kuma tabbas za a dinki ƙasar Sin baki ɗaya, lamarin da ba za a dakatar da shi ba. Yunƙurin nuna wa Taiwan goyon bayan da wasu Amurkawa suka yi ta hanyar ziyartar yankin, ba zai samu nasara ba. Kamata ya yi Amurka ta martaba manufar “ƙasar Sin ɗaya tak a duniya” da sanarwa guda 3 ta haɗin gwiwar Sin da Amurka, ta daina kau da kai kan batun neman ‘yancin kan Taiwan da kuma goyon bayan aikace-aikacen, ta kuma dakatar da ƙulla maƙarƙashiyar hana ci gaban ƙasar Sin bisa hujjar batun Taiwan.

Don haka, bai kamata a ƙasƙantar da aniyar al’ummar ƙasar Sin da ƙwarewarsu ta kiyaye ikon mulkin ƙasa da kuma cikakken yankunan ƙasa ba.

Fassarawa: Tasallah Yuan