Annobar COVID-19 ba za ta hana cigaban tattalin arzikin ƙasar Sin yadda ya kamata ba

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Tarukan manema labarai biyu da gwamnatin ƙasar Sin ta shirya da safiyar yau Litinin sun jawo hankali matuƙa daga bangarori daban-daban.

Taro na farko, wanda hukumar ƙididdiga ta ƙasar Sin ta shirya, ya fitar da wasu muhimman alkaluman tattalin arzikin ƙasar a watan Afrilun bana. Duba da yadda halin da ake ciki a duniya ke canjawa, gami da yanayin annobar COVID-19 a cikin gida, tattalin arzikin ƙasar Sin na kara fuskantar matsin lamba, inda kakakin hukumar ya yi nuni da cewa, dalilin kuwa shi ne tasirin da annobar ta haifar na gajeren lokaci, amma ba zai hana ci gaban tattalin arzikin ƙasar Sin yadda ya kamata ba.

Taro na daban, wanda gwamnatin birnin Shanghai ta shirya kan daƙile yaduwar cutar COVID-19 ya sanar da cewa, daga cikin yankuna 16 na birnin, akwai guda 15, waɗanda aka riga aka yi nasarar hana yaɗuwar cutar tsakanin al’umma, kana tun daga watan Yunin bana, za’a farfaɗo da harkoki da rayuwar yau da kullum a birnin. Bugu da kari, an kusan kawo ƙarshen yaɗuwar cutar a lardin Jilin dake arewacin ƙasar Sin, a yayin da kura ta fara lafawa a lardunan Henan da Jiangsu da kuma Zhejiang.

Duk waɗannan al’amuran sun shaida cewa, manufar gwamnatin ƙasar Sin ta taka rawa, wato daƙile yaduwar cutar da zarar an gano ta, abun da ya samar da tabbaci ga farfaɗowar tattalin arzikin ƙasa.

Maida rayuwa gami da lafiyar dan Adam a gaban komai, babban tushe ne na aikin dakile yaɗuwar cutar a kasar Sin. Duk da cewa matakan kandagarkin cutar za su iya haifar da tasiri na gajeren lokaci ga rayuwar mutane a wasu sassa, amma shaidu sun nuna cewa, muddin an hana yaɗuwar cutar, za’a iya kirkiro kyakkyawan sharaɗi ga ci gaban tattalin arziki.

Fassarawa: Murtala Zhang

By Editor