Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Jama’a na so na shiga wani babi a wannan makon amma ganin abubuwan da su ka biyo baya a kan zubar da jini a Gaza su ka saka na ga muhimmancin fito bayanan halin da a ke ciki a wannan yanki mallakar Falasɗinawa. Haƙiƙa a yau dai a duniya yankin Gaza na daga yankunan duniya da mutane ke zama a cikin zullumin hari da za a iya rasa rai ko samun raunuka a koyaushe. A kafafen labaru kafin ka ga wani labari na fitinar Yaman, Sudan ko Yukrain za ka ga labari kan Gaza. Labarin ka iya zama na gaskiya ko farafanda. Duk da yawan labaru kan Gaza hakan bai dakatar da yaƙin nan ba da ke neman cika shekara ɗaya cif da mutuwar fiye da falasɗinawa 40,000. Abun ma damuwar sosai shi ne waɗanda ke rasa ran su akasari ba mayaƙa ba ne ko a ce sojoji; mata ne da ƙananan yara. Idan yaki ya kai wannan tsanani to za a rasa matsuguni, abinci da ma sutura. Idan a ka nuna ma ka yanda sassan Gaza su ke a yanzu z aka ɗauka waje ne da a ka yi girgizar ƙasa don yadda gine-gine su ka rugurguje biyo bayan zuba mu su ruwan boma-bomai daga jiragen yaƙin Isra’ila.
Falasɗinawa na karakaina da ’yan kayansu a ka daga kudanci zuwa arewacin Gaza da ba lalle ba ne ko ma ina su ka gusa za su iya samun sa’ida. Hatta sansanonin gudun hijira ko ma asibitoci ba sa tsira daga hare-haren Isra’ila da ke zargin mayaƙan Hamas na amfani da bigirorin wajen samun mafaka. Za a fahimci cewa Isra’ila na son gamawa da duk wani abu da ya shafi Hamas ne kafin dakatar da yaƙin. Wannan ya sa a ke ganin duk da a na tattaunawa amma hakan bai sa sojojin Isra’ila dakatar da yaƙin ba. Hakanan ko ma ba a cimma wata yarjejeniya ba matuƙar Isra’ila za ta murƙushe Hamas gaba ɗaya to shikenan za ta iya dakatar da yaƙin da komawa mulkin mallaka kan yankin Falasɗinawa. Batun kafa ƙasar Falasɗinu gefe da ƙasar Isra’ila bai taɓa zama abun da Isra’ila ke marmarin sauraro ko amincewa da shi ba. Mu tuna marigayi Firaministan Isra’ila Yizhak Rabin ya rasa ran sa don sassaucin matsayi da ya ɗauka da ka iya kawo maslaha a fitinar Isra’ila da Falasɗinu. Ya nuna masu tsaurin ra’ayi na Yahudu ke iya maƙalewa kan mulkin Isra’ila da samun goyon bayan kawayen ƙasar da ba sa son ko tsaki a yi wa mahukuntan Tel Aɓiɓ kan duk matakan mulkin danniya da su ka ɗauka kan ƙasar Falasɗinawa. Da alamun duk ƙasar Larabawa da ke son zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki to ta rika takatsantsan wajen yi wa Isra’ila martani. Jodan da ke jikin Isra’ila tsundum kan fito ƙarara ta na cewa ba za ta bari a yi amfani da ƙasar ta wajen shiga yaƙin Isra’ila ba. Ma’ana Sarki Abdullah na Jodan na son aminta ƙasar sa daga mara baya ga kowane ɓangare ko zama mai hannu a fitinar in ka deɓe kiran a zauna lafiya ko a samu maslaha. Kazalika Sarkin da kan sa ya shiga jirgi mai saukar ungulu wajen aikin raba kayan agaji ga al’ummar Gaza.
Ba za mu ga laifin Jodan ba don ta na kare kan ta ne daga fushin ƙasashe masu ƙarfi da hakan zai iya kawo matsala ga sarautar ƙasar. Sa bakin Hezbollah a Jodan da ma yanda Sham ke hulɗa da Iran da karbar baƙuncin mayaƙa ya sa kai hare-hare ƙasashen da a kaikaice sun faɗa yaƙin na Gaza. Ba wata kasar Larabawa da za ta bugi kirji ta tallafawa Falasɗinawa ko Hamas da ƙarfin soja sai dai turawa Falasɗinawan agajin abinci da ko barguna. Ba za a iya cewa ƙasashen na Larabawa na bin ƙarin maganar in jifa ya wuce kai na ya faɗa kan kowa ba, haɗin kan Larabawan ba zai yiwu ba don yadda kowace kasa ke da muradi, tsarin mulki da yanayin mazauna ƙasar daban da saura. Tun yaƙin da Larabawa su ka yi tare kan Isra’ila a 1967 amma Isra’ila ta gama da su, ba su sake haɗa kai ba. An ma gano a yaƙin ma dama kan su ba a haɗe ya ke ba shi ya sa ba su samu nasara a yaƙin ba. Wasu bayanai ma na nuna da gangan su ka bari a ka samu nasara a kan su don makircin da su ke yi wa juna. Gabanin fara wannan sabon yaƙin na Gaza ma akwai yunƙurin diflomasiyya na ƙulla hulɗar jakadanci tsakanin Isra’ila da Saudiyya. A zamanin shugaban Amurka Donald Trump ma an samu ƙasashen Larabawa da su ka ƙulla hulɗar jakadanci da Isra’ila. Shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya nuna matukar takaicin sa a loakcin da ɗaukar cewa Larabawa ‘yan uwan su sun ci amanar su. Shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan wanda ba shugaban Larabawa ba ne ya nuna takaici kan matakin na waɗannan ƙasashen.
Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya sauka a Tel Aɓiɓ din Isra’ila don tattaunawa kan batun tsagaita buɗe wuta a yaƙin Gaza
Wannan ita ce tafiyar Blinken ta 10 zuwa gabar ta tsakiya tun fara gwabza yakin Gaza daga 7 ga Oktobar bara.
Bayan ganawa da jami’an gwamnatin Isra’ila ciki da Firaminista Benjamin Netanyahu, Blinken ya wuce Masar don cigaba da ƙarfafa muhimmancin amincewa da tsagaita wuta a makon nan.
Amurka, Masar da Katar da ke shiga tsakani har yanzu ba su samu dakatar da wannan yaƙin ba da har wannan shigowa ta Blinken a na cigaba da zubar da jinin Falasɗinawa a Gaza.
Shugaban Amurka Joe Biden ya tsara yarjejeniyar da ke da zummar dakatar da buɗe wuta, sako kamammu da musayar fursunoni da ma tsayar da yaƙin gaba ɗaya.
Ministan wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya tattauna da sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ta wayar tarho musamman kan neman dakatar da zubar da jini a Gaza.
Tattaunawar da ta gudana ta wayar tarho kazalika ta tabo shawo kan fitinar da ta hargitsa Sudan da kuma ƙasar Yaman.
Saudiyya na buƙatar a yi tsayin daka don ganin an samu maslaha a fitinar gabar ta tsakiya ta amfani da wannan kafa ta diflomasiyya.
Duk da Saudiyya ba ta cikin ƙasashe 3 da ke shiga tsakani wajen yarjejrniyar tsagaita wuta, amma matsayin ta na babbar aasar Larabawa da arzikin fetur ya sa muryar ta na da tasiri a fitinar.
ƙungiyar mayaƙan Hamas da ke mulkin Gaza ta soki kalaman sakataren wajen Amurka Anthony Blinken da ke cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza da a ka yi wa bita.
Blinken dai ya gana da jami’an gwamnatin Isra’ila kan yarjejeniyar inda kuma za a yi irin ganawar a Masar.
Babban jami’in Hamas Osama Hamdan ya ce sam ba wannan bayanan da Blinken ya fada ne a ka miƙa mu su ba.
Hamdan ya ce akwai wasu sassa masu harshen damo a cikin yarjejeniyar da ya nuna ba a gamsu da su ba.
Osama Hamdan wanda da alama ke zaune a Lebanon ya ce su na buƙatar a gabatar mu su yarjejeniyar da za a iya aiwatarwa ne.
Da furta waɗannan kalaman ko matsaya daga Hamas ya nuna akwai kura kan nasarar sabuwar yarjejeniyar ko sabon yunaurin dakatar da yaƙin Gaza.
A nata samun kwan gaba kwan baya kan neman tsagaita yaƙin Gaza yayin da Isra’ila ke cigaba da barin wuta.
ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon mai samun goyon bayan Iran ta kai harin ramuwar gayya matsugunin Ayelet Hashahar da ke arewacin Isra’ila.
Wannan ya biyo bayan mummunan farmakin da Isra’ila ta kai a yankin Nabatieh da ke kudancin Lebanon har mutum 10 su ka rasa ran su ciki da wata mata ’yar Sham da ’ya’yanta.
Isra’ila ta ce Hezollah ta harba rokokin KATYUSHA 55 kuma sojoji biyu sun samu raunuka.
Kazalika Hezbollah ta ce ta harba jirage biyu marar sa matuƙi kan wani mazaunin sojojin Isra’ila a Al-burj inda jiragen su ka ɗirkaki bigiren kai tsaye.
Haƙiƙa musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah a kan iyakar Isra’ila da Lebanon na ƙara ta’azzara.
A nan maimakon ma tsagaita yaƙin Gaza, sai a ka ga ƙarin fitina tsakanin sojan Isra’ila da Hezbollah a Lebanon. Sannan Isra’ila kan iya kai hari a kowane lokaci cikin ƙasar Sham don zargin ta na ɗaukar baƙuncin wasu mayaƙa da ke barazana ga Isra’ilar.
A can Bahar Maliya ma ƙungiyar ‘yan tawayen Houthi ba ta daina yunƙurin kai hare-hare kan muradun ƙasashe da ke hulɗa da Isra’ila ba. Amurka da Birtaniyya kan maida martani kan sassan da Houthi ke jagoranta a Yaman.
Kammalawa;
Ga dai yadda yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ke tangal-tangal duk da sawu na 10 kenan da sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ke yi kan fitinar. Ya dai kamata a san yadda za a yi a rage kashe wadanda ba su ji ba ba su kuma gani ba a Zirin na Gaza da su ka haɗa da jarirai, yara kanana, mata da kuma tsoffi. Gawwwaki sama da 40,000 na Falasɗinawa a sanadiyyar yaain sun isa ramuwar gayya matukar Isra’ila na son samun sauran mutane da za ta cigaba da gallazawa a yankin da sunan gyauron dangin ’yan Hamas.
