APC a 2023: Guguwar siyasa ta soma ruri a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Daga dukkan alamu, guguwar babban zaɓen gama-gari ta 2023 ta soma kaɗawa a ilahirin Nijeriya, saboda haka kowane ɗan siyasa, kama daga masu neman muƙaman jam’iyya ya zuwa masu neman a zaɓe su, don su jagoranci ko wakilci a matakai daban-daban sun soma neman hanyoyin samun cimma burinsu.

Jihar Kebbi ita ma ba a bar ta a baya ba, inda a can ma jam’iyyar APC mai mulki ta bi sawun sauran jihohin da APC ɗin ke mulki wajen zaƙulo mutanen da za su jagoranci jam’iyyar tun daga matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi, jiha zuwa tarayya, inda a waɗansu ƙananan hukumomin an yi sulhu, yayin da waɗansu kuma aka daidaita bayan da aka kai ruwa rana, waɗansu kuma har yanzu da sauran rina a kaba, saboda waɗansu su na ganin ba a yi musu adalci ba sanadiyyar cire sunayensu da aka yi, a ka maye gurbinsu da waɗansu da waɗanda a ke zargin ke riƙe da madafun iko a jihar suka yi, domin cimma ta su biyan buƙata, musamman wajen zaɓen fitar da gwani nan gaba.

Wani jawabi da shugaban jam’iyyar na riƙo na jam’iyyar a jihar, Alhaji Abubakar Muhammed Kana, ya yi a satin da ya gabata a wani taro da gwamnan jihar ta Kebbi da mutanenta  suka shirya a masaukin Shugaban Ƙasa da ke garin Birnin Kebbi ya janyo tayar da jijiyoyin wuya tsakanin ɓangarorin da ke yi wa juna kallon hadarin kaji a cikin jam’iyyar APC ta Jihar Kebbi, inda ya ke bayyana cewa, yanzu dai jam’iyyar APC ta riga ta kama hanyar samun nasara, domin tunkarar zaɓe mai zuwa, saboda dangane da babban taron jam’iyyar da aka yi dai an sami nasarar sulhu a ƙananan hukumomi 18 daga cikin 21 da ke akwai a jihar.

Hon. Abdullahi Muhammed Lamba (Dan Masanin Yauri) ɗaya daga cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Kebbi ya zanta da manema labarai, inda ya nuna rashin gamsuwarsa bisa ga yadda aka zo da wani tsari da ya ke cewa, “Ɗayan biyu ne; ko dai an bai wa waɗansu kwangilar wargaza jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ko kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Yobe Maimala Buni wanda ke riƙe da jam’iyya a ƙasa ne a ke neman a tozartawa ta hanyar yi wa jam’iyyar APC kafar ungulu, don kada ta kai ga samun nasara a jihar.

“Saboda haka mu ke ganin ya kamata mu fito mu gaya wa duniya cewa fa wannan taron da aka yi ba wai an shirya shi ba ne bisa ga tsari gaskiya ba, saboda sanin kowa ne ‘congress’ ya kan zo ne  bisa ga tsari na fuska biyu; ko dai a yi zaɓe tsakanin masu neman mukaman jam’iyya, inda inda duk wanda ke da katin shaidar zama ɗan jam’iyya ya kan fito ya zaɓi waɗanda ya ke so ko kuma a yi sulhu  tun daga matakan mazaɓa har zuwa na ƙasa, wanda yin haka shi ne mafi a’ala, ba wai waɗansu ’yan tsirarru su shige wani ɗaki su rubuta waɗanda su ke so, su cire waɗanda ba sa so ba bisa ga son rai ba, don kawai biyan tasu buƙatar.”

Sai ya yi kira ga Gwamnan Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, da ya sani fa irin waɗannan mutanen ba shi ko jam’iyya su ke so ba a’a,  su  ’yan a biyo yarima ne a sha kiɗa, “saboda yau idan aka wayi gari ba shi ne ke mulki ba, ba wanda zai ƙara gani a gidansa sai dai duk inda gwamnati ta juya su ma can za su juya. Saboda haka yana da kyau ya natsu a nemo duk waɗanda ke da ruwa da tsaki a jam’iyya daga dukkan ƙananan hukumomi 21 a jihar nan su zauna su yi abinda ya kamata.

“Amma maganar cewa, ƙananan hukumomi 18 daga cikin 21 da ke akwai a Jihar Kebbi wai an yi sulhu wannan maganar banza ce. Idan an yi sulhun a fa]i sunayen ƙananan hukumomin, sannan a ina aka zauna kuma yaushe, sannan kuma su wanene suka yi sulhun?” in ji shi.

Haka zalika Alhaji Kabiru Sani (Giant), ɗaya daga cikin shigabannin matasa a jihar ta Kebbi, ya bayyana wannan shirin da cewa, “wata yaudara da ce da kitsa saboda idan dai ana so a yi gaskiya ya kamata a baje ta a faifai kowa ya san abinda a ke ciki, saboda siyasar ba a hannun mutum ɗaya ta ke ba a Kebbi, akwai ɓangaren shi gwamna, Sanata Atiku Bagudu, akwai ɓangaren Sanata Adamu Aliero da kuma na Ministan Shari’a, Abubakar Malami, akwai sauran ’yan siyasa, sannan kuma kowannensu yana da na sa ra’ayi.

Amma maganar waɗansu su riƙa jan mutane kamar raƙumi da akala, wannan kam ba za mu lamunce ba, ba wani mutum ko gungun waɗansu da shige wani ɗaki su zayyana yadda su ke, sannan a ce kuma a zauna lafiya. Wannan kam ba za ta yiwu ba.”

Jam’iyyar APC dai a Kebbi ta daɗe cikin wannan yanayin na yi wa juna kallon hadarin kaji tsakanin ɓangarori, musamman dangane da wane ne zai gaji Sanata Atiku Bagudu a zaɓen 2023, wanda har ta kai ga ɓangaren gwamnati a na ƙuntatawa a fakaice ga mutanen da a ke ganin suna da wani ra’ayi saɓanin na ta tun kama daga ma’aikatan gwamnati zuwa ’yan siyasa, wanda a watannin baya ne ake ganin an yi wa tsohon shugaban jam’iyyar APC, Ark. Bala Sani Kangiwa, da Ma’ajinta, Alhaji Garba Musa T. Marina, da Sakataren Ku]i bi-ta-da-ƙulli yayin da  Dr Sani Dododo bisa ga wani hange da ya yi sai ajiye muƙaminsa na jami’in hul]a da jama’a na bisa zaɓin kansa.

A ɗaya ɓangaren kuma su ma talakawan jihar ƙorafi su ke yi a kan waɗannan da ke da haƙƙin tsayar da ɗan takara (watau ‘delegates’) inda su ke danganta duk wata uƙuba da su ke sha alhakin yana kan su saboda su ne a ke bai wa ɗan kuɗin da ba zai iya ɗaukar lalurar gidajensu ko da ta sati ɗaya ba, amma sai su jefa al’umma cikin u}ubar shekaru huɗu ko takwas ta hanyar zaɓa musu ɗan takarar da bai dace ba ko ba shi ne zaɓin al’umma ba.

Yanzu dai an zura ido a ga matakan da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar da ma a matakin ƙasa za su ɗauka, don shawo kan wannan matsala, wacce makamanciyarta ce ta dulmiyar da APC a maƙociyar jiharta, wato Zamfara, a 2019, inda rikicin cikin gida ya janyo Kotun Ƙoli ta kwace zaɓen APC, ta damƙa wa PDP, babbar jam’iyyar adawar jihar.