Matasa da madafun iko a Nijeriya

Daga NASIR S. GWANGWAZO
 
A wata hira da a ka yi da tsohon Shugaban Mulkin Soja na Nijeriya , Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, a cikin makon jiya lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ya yi iƙirarin cewa, bai dace a ƙara bai wa duk mutumin da ya wuce shekara 60 a duniya da haihuwa mulkin Nijeriya a zaɓen Shugaban Ƙasa da ke tafe na 2023 ba. Kalaman nasa sun janyo cece-kuce, amma fa ababen dubawa ne ƙwarai da gaske!

A Nijeriya, tarihi ya na cigaba da maimaita kansa, inda a ke mayar da matasan ƙasar saniyar ware a duk lokacin da a ka zo matakin rabar da muƙaman gwamnati, inda hakan ya fito a fili kan muƙaman da a ka rabar kuma a ka ajiye su matasan a gefe guda.

Hakan dai ya samu asali ne tun a Jamhuriyya ta Biyu, inda har yanzu a ke cigaba da yin hakan har zuwa yau a ƙasar.

Lamarin ya fi kyau a lokacin a mulkin mallaka da kuma lokacin da a ka samu mulkin kai a ƙasar, inda matasa daga masu shekaru 20 zuwa 30 a ke damawa da su a fannin mulki.
Hakan ya janyo jefa rayuwar matasan ƙasar a cikin halin tsaka-mai-wuya, inda wasu su ka gwammace su rungumi hanyar yin maula ko zama ’yan barandan siyasa a matsayin hanyoyin da za su taimaka wa kawunansu.

Mafi yawancin matasan rayuwar matasan Jamhuriyya ta Biyu ta sha bamban da rayuwar matasan yau, ganin cewar, rayuwar matasan na yau ba su da wata ƙwarewa ko isasshen ilimin boko.

Wannnan shi ne ra’ayin wannan jaridar, saboda ganin cewar, an mayar da matasan ƙasar saniyar ware a ɓangatren da ya shafi sanya su a cikin harkar gudanar da mulki.

Tun daga fannin shari’a da ɓangaren zantarwa, dukkan muƙaman da a ke rabarwa, sai ’yan mowa ne, amma ’yan bora an bar su a gefe, ba a damawa da su.

Alal misali; tantance sunayen waɗanda za a bai wa muƙaman ministoci da Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa da Majalisar Dattawa, don a tantance su tun a 2015 da kuma 2019, a kuma tabbatar da su, hakan ya nuna a zahiri matasan ƙasar a na ƙara ture su a gefe, inda dattawa su ke cigaba da ci da gumin matasan ƙasar ta fannin samun muƙaman gwamnati.

Duk dokar da ta bai wa matasa damar riƙe madafun iko a ƙasar da a ke kira a turance ‘Not-Too-Young-To-Run’ a duk waɗannan ranakun da kuma zuwa lokacin da a ka yi zaɓen gama-gari na 2019 a na ta gudanar da ayyukan siyasa, inda manyan jam’iyyun siyasun ƙasar, APC da kuma PDP, su ka gudanar da manyan gangami a kan lamarin da ya shafi mata da matasa.

An yi wa matasan alƙawura, inda su ka yi amanna cewar lokacinsu ne ya zo, inda kuma su ka bazama wajen nema wa ’yan takara masu goya mu su ,baya don su lashe zaɓuɓɓuka daban-daban.

Idan za mu iya tunawa, a lokacin Shugaban Nijeriya Buhari ya karɓi baƙuncin shugabannin ’yan }ungiyar ‘Not- Too- Young –To- Run’ a Fadar Shugaban Ƙasa da ke garin Abuja, ya shaida mu su dalilin da ya sanya ya sa hannu a kan ƙudurin  na ‘Not- Too- Young –To- To- Run’ har ya zamo doka, inda ya roƙe su da su ba shi goyon baya, don yin tazarce a karo na biyu na wa’adin mulkinsa.

Ya kuma yi mu su alƙawarin naɗa matasa da mata a muƙamai idan har ya lashe zaɓen, inda a saboda hakan ne tawagar matasa ’yan APC su ka gabatar da takarda ɗauke da sunayen matasa 100 da su ke buƙatar Buhari ya naɗa su a muƙaman ministoci da suran muƙamai, don ya yi duba a kai.

Takarda ce da matasan su ka tsara ta yadda ya dace, amma sai dai ba ta yi wani amfani ba. Amma abin takaici da kuma damuwa shi ne, babu mai shekara 40 zuwa 44 da a ka naɗa a muƙamin minista, inda hakan ya nuna a zahiri matasan ba su da wani wakilci a gwamnatin ta Buhari. Har su ma matan da a ka lasa wa zuma a baki an ajiye su a gafe, inda kawai daga ɗaya zuwa shida a wa’adin mulkin Buhari zuwa bakwai a ka  naɗa a muƙamai, mu na da yaƙinin har yanzu lamarin ba ta canja zani ba.

Tunda ya ke cewa, Buhari mai sauraron koke ne, mu na kira a gare shi da ya yi dubi a kan lamarin, saboda ganin yadda a ke mayar da matasan da kuma mata saniyar ware.

Babu wata tantama cewa, matasan ƙasar su na da hazaƙa kuma za su iya riƙe dukkan irin matakan gwamna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *