Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau
Ɗaruruwan magoya bayan ɓangaren Sen Kabiru Garba Marafa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a Jihar Zamfara sun bayyana sha’awarsu ta ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC tare da ƙin amincewa da bin Sanata Marafa da ya bar jam’iyyar a kwanakin baya.
Sun kuma bayyana goyon bayansu ga Sanata Abdulaziz Yari da ƙaramin ministan tsaro Hon Bello Mohammed Matawalle.
Da yake jawabi a madadin shugabannin jam’iyyar a ƙananan hukumomi 14 na ɓangaren Sanata Kabiru Garba Marafa, Alhaji Abdulkadir Mijin Yawa ya ce sun yanke shawarar cewa ba za su koma wata jam’iyyar Sanata Marafa ba domin, suna masu jaddada cewar za su ba da tasu gudunmawar domin samun nasarar jam’iyyar ta APC a shekarar 2027.
Alh. Abdulkadir ya bayyana ficewar Sen Kabiru Garba Marafa a matsayin wani gagarumin cigaba, yana mai cewa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban APC za su ɗore bayan ficewar sa daga jam’iyyar a jihar.
An gudanar da bikin ne a babban masaukin baƙi watau Command Guest Inn, dake Gusau babban birnin jihar a yau ranar Litinin.
Mijin Yawa ya bayyana Sanata Kabiru Garba Marafa a matsayin Wanda yaci amanar jam’iyyar APC a jihar, inda ya nuna cewa ficewar sa daga jam’iyyar ba za ta taba zama barazana ba illa kawo ingantattaciyar cigaba a tsakanin‘ya’yan jam’iyyar a jihar.
Da yake karɓar magoya bayan, shugaban jam’iyyar APC na jiha Hon. Tukur Umar Ɗanfulani wanda ya samu wakilcin sakataren jam’iyyar na jiha Hon. Ibrahim Umar, ya ba su tabbacin cewa za a tabbatar da daidaito a tsakanin su a jam’iyyar.
Ya buƙace su da su kasance masu bin doka da oda tare da bayar da gudunmuwar su domin samun nasarar jam’iyyar a 2027 a jihar.
Hon. Ɗanfulani ya bayyana cewa ficewar Kabiru Garba Marafa daga jam’iyyar zai kawo haɗin kai da cigaba a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da magoya bayan ta a jihar.
