
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya sanar da kammala warware matsalolin da suka haifar da yanke wuta a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da ke Jihar Kano.
A wata sanarwa daga KEDCO kamar yadda NigerianTracker ta ruwaito, al’amarin ya samo asalin ne daga ƙoƙarin raba layin lantarkin farfajiyar asibitin da ɓangarorin bada magani ga marasa lafiya daga sashen gidajen ma’aikatan asibitin.
An haɗa na farfajiyar asibitin da ɓangarorin kula da lafiyansa ne da tashar lantarki na 33kV Zaria Road, wanda ke bada wuta na jimillar sa’o’i 22 a kullum.
Hukumar gudanarwar AKTH ta ce barin sashin gidajen ma’aikata da na ɓangarorin lafiya yana jefa ɗorewar lantarki cikin haɗari a asibitin.
Duk da cewa KEDCO ta sha ƙoƙarin raba layin, hakan bai sa ta yi nasara ba saboda rashin bada haɗin kai daga hukumar gudanarwar, lamarin da ya haifar da tsaiko tare da samun ɗaukewar wutar akai-akai.
Don samun wadatuwar wuta a asibitin, KEDCO na cigaba da ƙoƙarin raba layin wutar domin inganta harkokin samar da lantarki a asibitin.
Haka kuma, yana da muhimmanci a sani cewa an biya kuɗin lantarkin da sashin gidajen ma’aikatan ya zuƙa duk da rashin ƙarfin wuta da kula da tattali daga ɓangaren KEDCO.
A wata takarda ranar 12 ga Agusta, 2025, jami’in kasuwanci na KEDCO, Muhammad Aminu Ɗantata ya shaida wa Daraktan Lafiya na AKTH shirin kamfanin na katse lantarki a sashin gidajen ma’aikata da wasu wurare marasa muhimmanci sosai, saboda rashin biyan kuɗin wuta a kowane wata yadda ya dace.
Lamarin da ya kai bashin wuta da ake bin asibitin Naira miliyan 949.8 zuwa watan Agusta 2025.
KEDCO ya kuma jaddada aniyarsa na cigaba da samar da wadataccen lantarki ga asibitin a matsayinsa na babban cibiyar kula da lafiya domin tallafa wa ayyukansa.
Don haka ya kirayi hukumar gudanarwar asibitin da ta ba su goyon baya wajen ganin an raba layin da ke haifar da tsaikon da kuma shawo kan matsalolin bashin.
