
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, ta musanta yi wa sananne kuma jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji rajista a matsayin mambanta.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce ɓata-gari ne suka ƙirƙiro da kati na bogi domin ɓata wa jam’iyyar suna.
“Hankalin mu ya kai ga wani katin jam’iyyar mu na bogi da ake yaɗa wa ɗauke da hoton Bello Turji, inda ake cewa an yi masa rajista a jam’iyyar mu. Wannan ba gaskiya bane,” inji sanarwar.
Yusuf ya ce, idan aka yi duba na tsanaki za a iya gane cewa katin na bogi ne.
“Babu wani mutum da za a iya yi wa rajista ba tare da lambar katin ɗan ƙasa ba wanda shi kuma Turji ba shi da ita. Don haka koƙari da wasu ke yi na shafa wa jam’iyyar bakin fenti bai yi nasara ba,” in ji kakakin jam’iyyar ta APC a jihar Zamfara.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wannan kati na bogi da ake yaɗa wa na alaƙa da wani Babangida Aliyu Shinkafi wanda aka dakatar a baya bayan-nan daga shiga shirin yin katin laturoni na jam’iyyar a jihar saboda wasu ɗabi’u mara kyau da yake nuna wa.
An kuma alaƙanta shi da katin ne saboda a shafinsa na Facebook a fara ganin katin jam’iyyar.
