
Daga BELLO A. BABAJI
Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara da mambobin majalisar dokoki ɓangaren Kakakinsu, Hon. Bashir Aliyu Gummi sun yi alla-wadai da umarnin kotu na kama ƴan majalisa tara.
A sanarwa mabanbanta da suka fitar a Gusau, jam’iyyar da ɓangaren majalisar sun zargi gwamnatin jihar da amfani da ɓangaren shari’a wajen wulaƙanta zaɓaɓɓun jami’ai da ƙoƙarin hana su yin aikin da aka zaɓe su a kai.
Sakataren labarai na APC a jihar, Yusuf Idris ya ce, Kotun Shari’a ta jihar ta umarci a kama ƴan majalisar ba tare da aika masu saƙon gayyata ba gabannin haka duk da cewa an miƙa batun da ake tuhumar su a kai zuwa ga Kotun Ɗaukaka ƙara dake Sakkwato.
Jam’iyyar ta ce, za ta cigaba da martaba hukuncin doka da ƙoƙarin ƙaurace wa duk wani al’amari da aka yi ƙoƙarin siyasantarwa musamman ganin yadda ƴan majalisar suka nuna damuwa akan matsalolin rashin tsaro da ke addabar yankunansu.
Ƴan majalisa ɓangaren Hon. Aliyu Gummi, ta hannun Hon. Aliyu Ango Kagara, sun koka game da matakin gwamnatin jihar, inda suka ce har yanzu su halastattun ƴan majalisa ne da ke wakiltar mazaɓunsu.
Ya kuma ce, barazana da nuna ƙarfin mulki ko ƙoƙarin yin amfani da shari’a wajen wulaƙanta su ba za su tsorata su ba.
Hon. Ango ya ƙara da bayyana zargin shirin kai masu hari tare da iyalansu, inda ya ce tuni suka sanar da jami’an tsaro da bada hujjoji da ke tabbatar da zargin nasu.
