Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa (NEC), ta amince da kafa Hukumar Bunƙasa Auduga da Kula da Masaƙu a Nijeriya.
Gwamna Hope Uzodima na Imo ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar a ƙarshen taron majalisar karo na 149 wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta, ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya bayyana cewa, domin ganin hukumar ta yi aiki yadda ya kamata, majalisar ta amince da ƙudirin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Mista Uzodima ya bayyana cewa za a zaɓo shugaban hukumar ne daga kamfanoni masu zaman kansu, inda ya ƙara da cewa hukumar za ta samu kuɗaɗen ne daga harajin shigo da kaya kan masaƙu.
“Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa, da dai sauransu, ta samu wakilci daga mambobin ƙungiyar da shugabannin ƙungiyar bunaasa Auduga, Masaƙu da Tufafi.
“Masu sana’o’in hannu ne masu zaman kansu da suka shiga sana’ar auduga da tufafi da masaƙu kuma gabatar da shawarwarin sun yi nuni da shawararsu kan yadda za a farfaɗo da sana’ar auduga a Nujeriya.
“Majalisar ta amince da gabatarwar kuma ta amince da kafa ofisoshi na kasa da na yanki na hukumar a kowane yanki na yanki shida na ƙasar don daidaitawa,” inji Mista Uzodima.
A nasa ɓangaren, Gwamna Douye Diri na Bayelsa, ya ce majalisar ta kuma samu shawara daga ministan kula da kiwon dabbobi kan dabarun bunƙasa sana’ar kiwo.
Ya ce, an gabatar da taron ne kan wani shiri na sauya sana’ar kiwo tsakanin shekarar 2025 zuwa 2030.
Ya ce, an gina dabarun ne a kan shirin haɓaka kiwo na ƙasa, wanda ake sa ran zai kawo sauyi a fannin samar da ayyukan yi, da fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da kuma zama ɗakin injuna domin samun kuɗaɗen shiga.
“Hasashen shi ne dabarun zai samar da tsakanin dala biliyan 74 zuwa kasa da dala biliyan 90 a wannan fannin nan da shekara ta 2035.
“Zai kasance haɗjn gwiwa kai tsaye tare da gwamnonin jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da masu zuba jari na kasashen waje a ƙarƙashin ingantacciyar gwamnatin tarayya,” inji Diri.
Ya ƙara da cewa, za a ba da fifikon zuba jarin zuwa wasu muhimman ginshiƙai guda biyar tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026.
Ya kuma ce, ginshiƙan su ne: Kiwon Lafiyar Dabbobi da Kula da Shiyyoyi, Ciyarwa da Ci Gaba, Gudanar da Albarkatun Ruwa, ƙididdigar Bayanai da Bunƙasa Sarkar Kiwon Dabbobi.
