APC na alfahari da ƙoƙarin Hon. Bamalum – Bukardima Lawan

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Bade a Jihar Yobe, Hon. Bukardima Lawan, ya ce jam’iyyar ta na alfahari da irin ƙwazon tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da matashin ɗan siyasa kuma Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, kan ilimi a matakin farko da na sakandire, Hon. Isa Bamalum Bashir.

Shugaban jam’iyyar ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da tallafin atamfofi kyauta ga mata masu ƙaramin karfi, wanda Hon. Isa Bamalum Bashir ya gabatar a cikin Makaranar Sakandiren Jeka-ka-dawo dake Gashu’a a jihar Yobe, ranar Jummu’a.

Ya ce ba wannan ne karon farko ba, a cikin lokuta da dama Hon. Bashir ya na aiwatar da raba kayan tallafi ga mata a yankin wanda suka haɗa da musulmi da Kiristoci, a matsayin bayar da tashi gudummawa wajen taimakon al’umma.

“Tallafin ya zo daidai lokacin da muke shirye-shiryen gobe Asabar, cikin yardar Allah za mu fita fagen zabe don mun sake zaɓar Gwamna Mai Mala Buni karo na biyu, tare da dukan yan majalisunmu na dokoki, inda a wannan karon zamu tabbatar jama’a sun bayar da cikakken haɗin kai don kai wa ga nasara.”

Shugaban jam’iyyar APC ya ce, “Ba wannan ne karon farko wanda Hon. Isa Ba-malum, yake gayyatarmu tare da sauran al’umma don mu shaidi raba wa mata masu karamin ƙarfi atamfofi, inda bai tsaya nan ba ya haɗa har da yan uwanmu Kiristoci.”

“Kuma a iya sanina, wannan matashin raba atamfofi sama da 977 ga mata masu ƙaramin ƙarfi. Wanda a matsayin mu na shugabanin jam’iyyar APC, mun yaba kuma mun gamsu da wannan hidima da yake wa al’umma a karamar hukumar Bade da jihar Yobe baki ɗaya.”

“Haka kuma sanannen abu ne, shima Gwamna Buni irin waɗannan ayyukan ne yake buƙata sauran yan siyasa su kwaikwaya, kuma wannan sune matasan da yake jin daɗin kasancewa kusa da shi masu ƙwazo da burin ci gaba. Mun yaba masa sosai a matsayin sa na matashi, mai kishin al’ummarsa, Allah ya saka maka da alheri.” Ya nanata.

A nashi ɓangaren, Hon. Isa Bamalum ya bayyana godiya da goyon bayan da yake samu daga Gwamna Mai Mala Buni, inda ya ce kowane lokaci ya na umurtar su wajen yin ayyukan alheri da kyautata wa al’umma.

“Sannan na keɓanci wannan tallafin ga iyayenmu mata ne bisa la’akari da na yi, mafi yawan lokuta da su ake gwagwarmaya a siyasa amma ba a faye kula su ba, sannan da irin yadda sune suka fi shan wahalhalu kuma ba a cika tunawa da su ba.”

“Sannan mun raba turamen atamfofi 623 a baya, jiya kuma mun raba wa ‘yan uwanmu Kiristoci 70 yau kuma 100 sannan yau za mu raba katin wasu atamfofi 100 ko sama da hakan, in Sha Allah.” In ji shi.