Zaɓe: Sojoji sun fara sintirin inganta tsaro a Jihar Borno

Daga SANI AHMAD GIWA

Gabanin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, Dakarun Sashen na 1 na Operation Haɗin Kai sun fara sintiri na karfafa gwiwa a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Dakarun tare da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Borno da sauran jami’an tsaro sun gudanar da wani gagarumin bajekoli a kewayen babban birnin Maiduguri, domin kawar da fargaba, da ƙarfafa ƙwarin gwiwar ‘yan ƙasar da kuma nuna shirin sojoji domin zaɓen ranar Asabar.

Babban kwamandan runduna ta 7 (GOC) da kuma Kwamanda ta 1 na Operation Haɗin Kai, Manjo Janar Waidi Shaibu ya umurci kwamandojin da ke yankin rundunar 7 na Operation Haɗin Kai da su tabbatar da cewa dakarun da ke ƙarƙashin rundunar sun ci gaba da kasancewa masu sana’a da siyasa a lokacin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jiha a jihar Borno.

Janar Waidi ya bada wannan cajin ne yayin da yake jawabi ga kwamandojin runduna ta 7 da ke Maimalari Cantonment, Maiduguri a ranar Alhamis, 16 ga Maris, 2023.

Hukumar ta GOC ta tabbatar da cewa, wannan cajin ya yi daidai da umarnin Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, ga dukkan kwamandojin ƙasar nan domin gudanar da aiki cikin tsari na mataki na 2 na Operation Safe Conduct.

Janar Shaibu, wanda ya yaba wa rundunar ta COAS ga sojojin, kan yadda suke gudanar da ayyukan tsaro a duk lokacin da ake gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya, ya kuma gargaɗi duk wanda ke ƙarƙashinsa da su guji duk wani nau’i na tsokana, ko yin zamba wanda zai iya kawo cikas ga tsaro a rumfunan zaɓe, yana mai jaddada buƙatar samar da yanayi mai inganci da tsaro a lokacin aikin.

Janar Shaibu ya kuma buƙaci sojojin da su bi ƙa’idojin da aka gindaya da ɗa’a ga ƙa’idojin aiki, yana mai nuni da cewa duk wani saɓani zai haifar da mummunan sakamako.

Ya buƙaci kwamandojin da su ƙara zage damtse wajen bayar da goyon bayan samar da tsaro da ya dace da tsarin mulki ga hukumar da ke kan gaba wajen gudanar da zaɓe, inda ya ce a shirye suke wajen mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani lamari idan buƙatar hakan ta taso.