APC na takura wa ‘yan adawa – Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Jam’iyyar APC mai mulki da takura wa ‘yan adawa a Nijeriya.

Ya yi wannan martanin ne bayan kalaman da Kakakin Yaɗa Labarai na APC, Feliɗ Morka, ya yi kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen da ya gabata, Peter Obi.

A ranar Litinin, Obi ya yi zargin cewa saƙon sabuwar shekararsa game da halin da ƙasar ke ciki ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jawo barazana ga rayuwarsa da iyalinsa.

Ya bayyana wannan ne bayan da Morka, a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise , ya ce: “Peter Obi ya karya doka sau da yawa, kuma duk abin da ya same shi yana da alaka da abubuwan da ya aikata.”

Da ya ke mayar da martani, Atiku a wani saƙo da ya wallafa ta X a ranar Talata, ya ce wannan lamari “yana nuna wata hanyar da ba ta dace ba da wannan gwamnatin ke amfani da ita wajen tunkarar ‘yan adawa.”

By ukarofi