APC ta dakatar da tsohon Ministan Buhari Aregbesola

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar APC, reshen jihar Osun ya dakatar da Rauf Aregbesola, tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, saboda zargin ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya.

Dakatarwar ta na ɗauke ne a cikin wata wasiƙa da Tajudeen Lawal da Alao Kamoru, shugaban jam’iyyar da sakatarensa, suka sanya wa hannu.

An aika wasiƙar zuwa ga shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, tare da kwafin ta da aka bai wa manema labarai ranar Talata a birnin Osogbo.

A cewar wasiƙar, dakatarwar Aregbesola ta biyo bayan zargin ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya da kwamitin zartarwa na jam’iyyar na ƙaramar hukumar Ilesa East ya gabatar a kansa.

Ta ce kwamitin zartarwa na jihar na jam’iyyar, bayan nazarin zarge-zargen tare da la’akari da sashe na 21(3)(ɓi)(c) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, ya dakatar da Aregbesola har zuwa lokacin da kwamitin ladabtarwa zai kammala bincike.

Wasiƙar ta kuma bayyana cewa an kafa kwamitin ladabtarwa don bincika zarge-zargen tare da ba Aregbesola damar ya mayar da martani kan zargin da aka yi masa da ke sashe na 21(2) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Ta ce zarge-zargen sun haɗa da; ƙirƙirar ɓangaranci a cikin jam’iyya ta hanyar samar da ƙungiyoyi kamar Omoluabi caucus, kafa wasu tsare-tsare na daban a cikin jam’iyyar, aiki tare da jam’iyyun adawa, yin furuci na fili kan shugabannin jam’iyya da suka haɗa da shugaban ƙasa Bola Tinubu.