APC ta lashe zaɓen Sanatan Kudancin Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Babban jami’in hukumar INEC, Dr. Abacha Melemi na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gashua (FUGA), shi ne ya jagoranci zaɓen 2023 a lokacin da yake sanar da sakamakon a yau a garin Potiskum.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta INEC ta ayyana Sanata Ibrahim Mohammed Bomai a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda ya gudana yau Asabar, a Yobe ta kudu.

Sanata Bomai na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 69,596 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Hon. Halilu Mazagane, mai ƙuri’u 68,885. Sauran sun haɗa da Hon. Yerima Adamu na ADC 652, Hon. Jauro Ishaku – LP 471, Isa Musa – NNPP 3,277 da Maisambo Barde na jam’iyyar YPP mai kuri’u 448.

A sa’ilin da yake bayyana sakamakon zaben, a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (FCE. T) dake Potiskum, Dr. Abacha Melemi ya ce, “Ni ne Abacha Melemi, jami’in hukumar INEC mai kula da zaɓen 2023 na mazabar Sanatan Yobe ta Kudu, zaɓen da ya gudana ranar 15 ga watan Afrilu, 2023, wanda ya nuna Bomai Ibrahim Mohammed na jam’iyyar APC shi ne ya cika dukan ƙa’idojin da doka ta tanada, saboda haka na ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.”

A lokacin da yake jawabi jim kaɗan da bayyana sakamakon, Sanata Ibrahim Mohammed Bomai ya nuna godiyarsa ga al’ummar Yobe ta Kudu bisa gagarumin goyon bayan da suka ba shi wajen samun wannan nasara da ya yi.

Har wa yau, Bomai ya bayyana godiyarsa da jinjina wa Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC dangane da goyon bayansu zuwa ga samun nasararsa.