Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Bikin mauludi na takutaha ya jima ana gudanar da shi a Birnin Kano da jihar baki ɗaya, inda ake yin hawa da kuma shagulgula. Wannan ya sanya Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Kano ya bi sahun masu hawa Goron Dutse wajen bikin Hawan Takutaha, inda ya tattauna da malamai da mabiyan Mauludi kan muhimmancin wannan rana ta zagayowar haihuwar Shugaban Halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Wannan al’ada ta shafe ɗaruruwan shekaru tana gudana daga ranar 12 ga Rabi’ul Awwal zuwa 19 ga watan, wacce a Kano aka fi sani da Takutaha.
A wannan rana, jama’ar Kano, musamman matasa maza da mata, kan fito tun daga safiya har zuwa dare, daga gabas da yamma, kudu da arewa, zuwa Goron Dutse da Dala. A wurin za ka tarar da manyan tutocin gargajiya, tarurruka, gangami, waƙoƙin yabon Manzon Allah da sauran shagulgula. Wasu na hawa da keke ko abin hawa, wasu kuma da ƙafa, yayin da wasu ke rerawa da a waƙen baka. Wannan al’ada ce wadda ake gudanarwa cikin girmamawa da farin ciki.
Malam Muhammad Ansar Ibrahim, babban malami a Madabo kuma Shugaban Makarantar Khalifofin Rashidun a Kano, ya bayyana cewa asalin Hawan Takutaha ya samo asali ne daga gidan Madabo, inda babban malami na Madabo ya fara shi domin nuna farin ciki da haihuwar Manzon Allah. Ya ce ana gudanar da shi ne domin faɗakar da al’umma kan tarihin Annabi (SAW), nagartarsa, jarumtarsa da kyawawan halayensa, domin a koyi da su.
Sheikh Usman Warshu, a nasa jawabin, ya yi martani kan ra’ayoyin wasu da ke cewa Mauludi bidi’a ne. Ya ce duk wanda ya binciki littafan Ibn Taimiyya zai samu inda ya bayyana cewa Sahabbai sun taru suka yi murna da haihuwar Manzon Allah a gidan Arƙam bn Arƙam, inda suka ci abinci tare da nuna farin ciki. Haka kuma, Sheikh Warshu ya jaddada cewa Alƙur’ani ya umarci musulmi da su yi farin ciki da falalar da Allah Ya ba su, kuma mafi girman falala ita ce haihuwar Manzon Allah.
Ya ƙara da cewa kalmar “bidi’a” tana da nau’o’i: Akwai bidi’a wajiba, bidi’a mustahabba, bidi’a makruha da bidi’a haram. Misali, a da Sahabbai suna yaƙi da makami irin na baka da takobi, amma yanzu an ƙirƙiri bindigogi da wuta. Yin amfani da su don kare Musulunci ma bidi’a ce, amma bidi’a wajiba. Saboda haka, ya ce ba daidai ba ne a wuce gona da iri wajen fassara bidi’a, domin akwai bidi’ar alheri kamar bikin Mauludi.
A wani ɓangare kuwa, Khalifa na Zawiyar Malam Adhama a Kano, Sheikh Ibrahim Abdurrahim, ya bayyana cewa matsayin Manzon Allah ba zai iya gushewa daga duniya ko lahira ba, domin shi ne zai fara yin ceto a lahira. Ya ce ana gudanar da Mauludi domin faɗakar da al’umma kan tarihin Annabi da koyarwarsa, tare da bayar da abinci da sadaka ga mabuƙata. Sai dai ya gargaɗi jama’a da cewa ya zama wajibi a gudanar da Mauludi bisa tsarin shari’a, ba tare da ƙara abubuwan da suka saɓa ba.
Shi kuwa Sarkin Dillalan Kano, Alhaji Mustapha Aro, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka gudanar da Hawan Takutaha lafiya, aka kuma sauko lafiya. Ya yi kira ga dillalan Kano da su yi koyi da halayen Manzon Allah wajen kyakkyawar mu’amala da maƙwabta, gaskiya a ciniki da kuma kyautata zamantakewa.
Ita kuwa Makarantar Ma’ahad Sunusi Mai Turare, ƙarƙashin jagorancin Malam Abba, ta gudanar da saukar Alƙur’ani a ranar Takutaha domin haɗa murnar Mauludi da saukar Alƙur’ani a lokaci guda. Wannan ya ƙara armashi, inda aka samu halartar manyan baƙi irin su Alhaji Aminu Sani Turare, Alhaji Garba Mai Rawani, Shehu Anjilalini da sauran fitattun shugabanni da malamai.
A ƙarshe, Kwamishinan Al’amuran Addini na Jihar Kano, Sheikh Tijjani Sani Auwalu, tare da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, sun bayyana jin daɗinsu da yadda aka gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali. Sheikh Tijjani ya ce duk wani yunƙuri na kawo cikas ga al’amuran da suka shafi Annabi ba zai taɓa yin nasara ba, domin al’amuransa koyaushe suna tafiya ne da kariyar Allah.
