Aski ya zo gaban goshi!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Akan ce idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi, amma da alamu irin askin wanzamai na asali a ke magana masu aiki da ask aba irin waɗannan masu aski a shagunan zamani a na kallon akwatin talabijin ko a kunna faifan kiɗa a cikawa mutane kunne.

Manufa a nan ina son magana kan kammala mulkin shugaba Buhari na tsawon shekaru 8 da kuma shirin shigowar sabuwar gwamnati da Insha Allah kafin mu dawo sabon babi an fara ƙidayar kwanaki a sabuwar gwamnatin. Shin ko jami’an gwamnatin mai barin gado na son tafiya ko so su ke yi a cigaba da tafiya da su lokaci ne zai nuna.

Mulki ai ya na da daɗi sai dai ya na da nauyi. Nauyin nan kuwa ko ba a iya saukewa a duniya ba lalle kuwa za a sauke a kiyama. Me ya kamata duk ɗan ƙasa nagari ya yi shi ne kishin ƙasarsa da ba da gudunmawar yanda za ta samu cigaba da tasiri a tsakanin sauran ƙasashe.

Ko an ji daɗin gwamnati ko ba a jib a ƙasar dai ita ta haɗa kowa don haka duk dauriyar da za a yi ƙasar ta dore ko bayan ba ma nan ya dace a yi hakan. Ai ma kusan duk waɗanda su ka karɓo ’yancin ƙasar ba sa doron duniya amma da yawan su sun bar tarihi mai kyau musamman na ƙasa da za a yi alfahari da ita.

Shugabanni daga jama’a su kan fito don haka in ba a dace a yau ba gobe za a iya dacewa. In ma an yi saɓani da sa’a irin ƙasar da mu ke son gani ba ta tabbata a zamanin rayuwarmu ba to in Allah ya yarda masu zuwa nan gaba za su shaida haka. In hakan ne ya fareu ya dace duk lokacin da za a shaida hakan ya zama sun tuno da mu da yi ma na addu’a don tubulin da mu ka aza mu ka bari don su amfana.

Ai kamar shuka bishiyar dabino ne da ba lalle wanda ya shuka ko dasa ya ci moriya ba in ba don dabarun zamani na samar da iri da zai bunqasa da wuri. Duk da haka in mun lura bishiyar dabino kan daɗe a duniya kuma wasu bishiyoyin ma a unguwanninmu haka nan mu ka tashi mu ka gan su don haka waɗanda su ka dasa su zai yi wuya in su na raye.

Za mu iya ƙaddarawa ma sun daɗe da barin duniyar. Alheri ya na da kyau duk in ka shuka shi ko ba ka girba ba wani na ka zai amfana. Duk jami’an gwamnati kama daga shugaba Buhari na duba irin abubuwan da su ka shuka a tsawon shekarun nan. Kakakin shugaba Buhari Femi Adeshina ya ba da sanarwar wani shiri da sashin na labaru na fadar Aso Rock ya shirya a faifan bidiyo kan mulkin shugaba Buhari a tsawon minti 55 da an nuna ko za a cigaba da nunawa a gidajen talabijin ciki da NTA.

Haƙiƙa ba za a yi mamaki ba in duk shirin ya ambaci alherin gwamnatin Buhari ne daga farko har ƙarshe. Ai masu abu da abun su su ka shirya shirin don haka zai yi wuya hatta masu sharhi a samu waɗanda za su yi suka ko da mai ma’ana ce a shirin. Ina ma a ce na samu na kalla da na ba ku labarin yadda shirin ya ke. Duk bayanai sun nuna shugaba Buhari zai nufi Daura ne mahaifarsa bayan sauka daga karaga inda hakan ya zama al’adar shugabanni in sun sauka kamar yadda tsohon shugaba Jonthan ya yi a ranar 29 ga watan Mayu 2015 inda daga Abuja ya nufi garinsu Otuoke a jihar Bayelsa.

Gaskiya duk yadda mutum zai gab akin mulkin dimokraɗiyya to akwai abun burgewa a cikin sa kuma shi ne wa’adi. Ba kamar mulkin soja da sai ranar da sojoji su ka yi niyya za su sauka ba ko mulkin mulukiyya inda sai ma rai ya yi halinsa bisa ala’ada za a samu sauyi nan ma sauyin sai dan gado, dimokraɗiyya ta na da iya adadin shekarun da a ke yi a kan mulki kuma dole in shekarun su ka cika a sauka matuƙar ba a samu sauyi a tsarin mulki ba.

Abun takaicin dimokraɗiyya shi ne akasarin masu hawa karagar musamman a nan Afurka ba waɗanda ke son sauka ba ne kuma in sun sauka ba lalle ne wani na daban daga danginsu ’yan jari hujja ba ya iya hawa karagar. Mu duba yadda wasu ma kan yi mulki har sau biyu daga na soja su rikiɗe farar hula su sake shantakewa kan kujera jami’an tsaro na yi mu su hidima dare da rana kamar ba haihuwarsu a ka yi kai kamar ba sa bawali ko bahaya. Kai ɗan Adam na da abun faɗa.

Mun tuna yanda tsohon shugaba Obasanjo ya dawo mulki daga 1999-2007 bayan mulkin soja da ya yi ya sauka a 1979. A saukarsa a farar hula sai ya yi ta faɗi tashin lalle sai an gyara tsarin mulki don ya zarce ya cigaba da sukuwa a karagar mulkin Nijeriya har wataƙila rai ya yi halinsa! Allah dai bai ba shi dam aba, don Majalisar Dattawa ƙarƙashin Ken Nnamani da ta wakilai ƙarƙashin Aminu Masari sun kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da yunƙurin duk da zarge-zarge da a lokacin a ka riƙa cewa an kashe maƙudan kuɗin a fitar hankali har da kusan kyautar gidaje.

Gaskiya in har mu na son ƙasarmu ta cigaba sai talakawa sun jajirce sun kaucewa biyewa mamayar ‘yan jari hujja sun koyi cewa ba mu amince da babakere ba. Duk wanda bai kyauta mu su su daina hulɗa da shi ba lalle ba dole. Goyon bayan da marar sa adalci ke samu daga talakawa don samun na cefane ke sa su yin abun da su ka ga dama.

Yaya za a zaɓi mutum ko kuma ko ta yaya ya hau kujera tun da ta siyasa ce sai ya juye ya zama ba mutum ba wai shi ba daidai da sauran mutane ya ke ba. Duk alfaharin mutum indai ba mutane ai aikin baban giwa ne mulki kai ba ma zai yiwu ba.

Batun taɓarɓarewar tsaro da kuma ƙuncin tattalin arziki su ka fi zama abubuwan tattaunawa a tsakanin ’yan Nijeriya musamman talakawa kan mulkin shugaba Buhari na shekaru 8.

Da alamu mutane kan yi magana a kan waɗannan al’amura ne don su na cikin abubuwan da shugaban ya yi alƙawarin gyarawa in ya dare kujerar shugaban ƙasa.

Irin bayanan jama’a kenan da wasun su duk da ƙalubalen da a ke fuskanta kan ce a yi fatan alheri ko addu’a don samun sauƙi.

Ga Farfesa Usman Yusuf da kan ba da gudunmawa ga lamuran tsaro, ya zama mai muhimmanci a nazarci asalin abubuwan da su ka haddasa matsalar rashin tsaron da ya addabi wasu jihohin arewa maso yamma. Matuƙar ba a gano ko mai da hankali kan tushen fitinar ba to haka za a yi ta fama yau fari gobe tsumma.

Fred Manjack tsohon ma’aikaci ne a ma’aikatar labaru wanda ke da lalurar kafa kuma ya jajirce har ya yi ritaya, ya nuna ƙorafin rashin samun kulawa ta musamman ga mutane irin sa ba kamar ma waɗanda ko aikin ba su da damar yi. Manjack ya ba da labarin wata ziyara da su ka je wata ƙasa inda da saukarsu a filin jirgi a ka kawo keken guragu a ka dauke shi har masauki; amma lokacin da ya dawo Nijeriya haka ya yi ta dogara sandarsa har inda ya samu taksi a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

A wata amsa da ya bayar kan tsaro da ma ƙuncin rayuwa, mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya yi tsayin daka wajen rike amanar ƙasa don haka jama’a ya dace kowa ya riqa ba da hadin kai don samun cikakkiyar nasara. Kan tsaro Shehu ya ce ba daidai ba ne a riƙa sanya siyasa a ciki don ai lamarin ya shafi kowa.

Wani sauyi a nan a ƙarshen gwamnatin Buhari shi ne rage dora matsalolin ƙasar kan tsohuwar gwamnatin PDP inda gwamnatin ta APC kan ce ta ware maqudan kuɗi a kowane ɓangare don kawo gyaran da ta yi alƙawari.

Kammalawa;

Shin mutane za su yi kewar shugaba Buhari ko ba za su yi ba, ya na da kyau a kyautata fata cewa yau tafi jiya alheri hakanan gobe ma ta fi yau kyau. Duk lokacin da ka ji an tuna bara to ba a ji dadin bana ba. A yanzu dai gaskiyar magana talakawa ba sa kewar tafiyar shugaba Buhari don yadda su ke ganin ƙuncin da su ke ciki na rayuwa ya ƙara ta’azzara ne kuma sun yi ta jajircewa don in shugaban ya samu dama ya bi matakan da rayuwarsu za ta inganta. Shugaban dai mai barin gado ya ce ba zai ci amana ba kuma ba zai bari ya na gani a ci amana ba. Shin ya cika alƙawarin?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *