Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ɗan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya sake jaddada aniyarsa ta magance matsalar rashin tsaro, yana mai cewa yunƙurin da ake zargin ana yi na kawo cikas ga kamfen ɗin jam’iyyarsa ba zai hana ta gudanar da ayyukanta gabanin babban zaɓen 2027 ba.
Rahoton News Point Nigeria ya bayyana cewa Atiku ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da kamfen ɗinsa na shugaban ƙasa a Sakkwato, inda ya buƙaci ’yan Nijeriya su mara wa ADC baya tare da zaɓen jam’iyyar a babban zaɓen da ke tafe.
Wannan furuci nasa ya zo ne kwana guda bayan ya zargi gwamnatin Jihar Sakkwato da jami’an tsaro da shirin kawo cikas ga taron kamfen ɗin, inda ya yi zargin cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tana ɗaukar nauyin wasu masu zanga-zanga domin tayar da hargitsi da samar da yanayin da za a iya amfani da shi wajen sanya dokar hana fita.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Talata, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma zargi gwamnatin jihar da hana ADC damar amfani da wuraren taron jama’a da kuma samar mata da kayan aikin gudanar da gangamin. Ya bayyana matakan a matsayin yunƙurin hana jam’iyyar adawa damar fafatawa cikin adalci.
Daga bisani, DSS ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin Atiku, inda ta ce Darakta-Janar na hukumar ne ya bayar da wannan umarni, duk da cewa hukumar ta bayyana zargin a matsayin wanda bai yi daidai da yadda take gudanar da ayyukanta ba.
A martaninta, hukumar ta ce jami’anta suna bayar da kariyar tsaro ga ’yan siyasa daga dukkan jam’iyyun siyasa. Ta kawo misalin lamarin ɗan takarar gwamnan ADC a Sakkwato, Mannir Daniya, wanda jami’anta suka ce sun kwashe zuwa wuri mai aminci bayan an kai masa hari a ranar 31 ga Oktoba.
Duk da ce-ce-ku-ce da ya dabaibaye batun, Atiku ya ci gaba da gudanar da ƙaddamar da kamfen ɗin, inda ya bayyana cewa babu wani yunƙuri na kawo cikas da zai hana jam’iyyarsa zuwa ga al’ummar Sakkwato.
Ya bayyana cewa an zaɓi jihar ne da gangan domin ƙaddamar da kamfen ɗin saboda muhimmancin tarihinta da kuma matsayinta na jihar da ta yi fice wajen zaman lafiya.
ɗan takarar ADC ya tuna da alkawuran da ya yi wa al’umma a lokacin kamfen ɗinsa na baya, yana mai cewa ya dawo ne domin sake jaddada waɗannan alkawura, musamman na magance matsalar rashin tsaro idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu a ranar zaɓe domin kaɗa ƙuri’unsu ga ADC, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa kan manufar siyasar jam’iyyar.
Gangamin ya zama farkon gudanar da ayyukan kamfen ɗin Atiku na neman shugabancin ƙasa a Sakkwato gabanin babban zaɓen 2027.
