Firaministan Australiya, Anthony Albanese, ya sanar da cewa, gwamnatin ƙasar za ta amince da ƙaddamar da ƙasar Falasdinu a matsayin ƙasa mai cikakken iko a zauren Majalisar ɗinkin Duniya da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa.
Wannan mataki yana nuna sabon salon manufofin Australiya na tallafa wa zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasa biyu a rikicin Isra’ila da Falasɗinu.
ƙungiyoyin goyon bayan Falasdinu da kuma ‘yan siyasar jam’iyyar Labour, musamman ɓangaren da ke goyon bayan Falasɗinu, sun yi maraba da wannan shawara. Sai dai kuma, Isra’ila da wasu ‘yan ƙasar sun nuna rashin jin daɗinsu, suna ganin hakan zai iya ƙara tsananta matsalolin tsaro.
Ministan Harkokin Waje na Australiya, Penny Wong, ta bayyana cewa wannan matakin zai taimaka wajen kawo adalci da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
Bayanin Albanese ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da tashin hankali a Gaza da kuma ƙaruwar rikici a Yammacin Kogin Jordan.
Wannan mataki na Australiya zai iya shafar dangantakar ƙasar da Isra’ila da sauran ƙasashen duniya masu ruwa da tsaki a yankin.
