01
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar masu goyon bayan shugabanci na gari a Birnin-Gwari, wato 'Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance', ta yi tir da abinda ta kira da kalaman karairayi da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya ƙirƙira akan tsarin zaman lafiya na Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari a jihar. Ta bayyana kalaman nasa a matsayin 'kare mai haushi ga wata' duba da cewa sun ci karo da abinda ya bayyana a zahiri ga al'umma a yankin. A wata takarda da Shugaban ƙungiyar, Ibrahim Abubakar NaGwari ya fitar, ƙungiyar ta bayyana kalaman El-Rufa'i na cewa Gwmanatin jihar…
