Babaji

5698 Posts

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Sufeton ƴan sanda, Solomon Arase ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Sufeto-Janar na ƴan sanda, Solomon Arase ya rasu. Wani daga ciki mataimakansa ya tabbatar wa Blueprint rasuwar marigayin a yau Lahadi. A watan Afrilun 2015 tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya naɗa shi a muƙamin, sannan ya yi murabus a 2016. Ya kuma cigaba da yi wa ƙasa hidima a matakai daban-daban tun daga lokacin. Haka ma a watan Janairun 2023, ƙarƙashin shugabancin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, an naɗa shi Shugaban Hukumar Ƴan Sanda PSC, inda ya riƙe muƙamin har zuwa watan Yunin 2024.
Read More

Yadda kaso 59 ya zama na yara daga ɓatattun ƴan Nijeriya 23,659 – Rahoto

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin ƴan Nijeriya guda 23,659 suka ɓata da har yanzu ba a same su, lamarin da ya jefa iyalai 13,595 cikin ƙunci, kamar yadda rahoton kwamitin ƙasa-da-ƙasa na tallafi (ICRC) ya bayyana. Jami'in ICRC, Benson Lee ya fitar da rahoton a Yola, kamar yadda rahotanni suka bayyana inda yayin jimamin ranar tunawa da mutanen da suka ɓata da tallafa wa iyalansu. Lee ya bayyana cewa, yawan ɓatar mutane a Nijeriya na da alaƙa mai ƙarfi da yawan rikici tsakanin al'umma a matsanancin rashin tsaro a shiyyar Arewa-maso-Gabashin Nijeriya. Ya ce, kaso 67 na al'amarin…
Read More

NAHCON ta fitar da tsarin harkokin Hajjin 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta sanar da ranakun kammala shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2026. NAHCON ta bayyana haka ne a shafinta na X ranar Juma'a, inda ta ƙulla yarjejeniya ta MoU tsakaninta da hukumomin Saudiyya cewa za a fara shirye-shiryen hajjin a watan Nuwamban 2025. Ta ce, zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2026 za a rufe biyan kuɗin rajistar zuwa aikin hajji ga maniyyata. Daga nan a ranar 1 ga Fabarairu, 2026 kuma za a rufe shigar da kwangilolin sufuri da masauki a shafin yanar gizo na Nusuk Masar. Hukumar…
Read More

Shettima ya halarci ɗaurin auren jikar marigayi Buhari a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya halarci ɗaurin auren Halima Junaid, wadda jikar marigayi tsohon shugaba Muhammadu Buhari ce da angonta Walid Mu'azu, wato ɗan Iyan Katagum. An gudanar da ɗaurin auren ne a masallacin Juma'a na Yahaya Road da ke Unguwar Rimi a Birnin Kaduna. Daga cikin waɗanda suka raka Mataimakin Shugaban ƙasar akwai; mataimakin shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia; Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Lawal; Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali; da Ɗan majalisa Lawal Zannah. Haka kuma Shettima shi ne wanda ya bada auren amaryar yayin da…
Read More

Bayan shekara biyar da tsare Zainab Aliyu a kurkukun Saudiyya, NDLEA ta fallasa yadda ake yi wa masu tafiya ƙasar ibada cune

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta fallasa wata dabar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke ayyukansu a fannin sufurin jiragen sama na Nijeriya. Ta kuma zarge su da sanya ababen maye a kayan maniyyatan aikin hajji ko umara domin jefa su a matsala yayin da suka isa ƙasashen waje. NDLEA ta fitar da rahoton ne kwanaki kaɗan da hukumomin Saudiyya suka tsare wasu masu umara daga Nijeriya da suka haɗa da Maryam Hussaini Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da kuma Abdulhamid Sadiq bisa zargin su da safarar miyagun ƙwayoyi. Lamarin da…
Read More

Amurka ta ƙi bai wa wakilan Palesɗinu biza gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Ma'aikatar harkokin waje ta Amurka ta tabattar da soke bizar shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da wasu jami'an Falasɗinawa su guda 80. Wannan mataki dai zai hana Mahamoud Abbas halatar taron ƙoli na MƊD da za a yi a watan Gobe a birnin Washington na Amurka. A taron ne dai aka yi tunanin ƙasashe da dama sun ƙudiri anniyar amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴanci, wanda shi ne babban burin mutanen yankin. Isra'ila ta dage kai da fata cewa bai kamata a ba Falasɗinu ƴancin zama cikakkiyar ƙasa ba, kuma tana samun goyon bayan Amurka, kamar yadda BBC Hausa…
Read More

2027: Jonathan ba zai iya kada Tinubu ba – APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC a Jihar Legas ta ce ta fahimci akwai yiwuwar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya tsaya takara a zaɓen 2027 da ke tafe. Rahotanni sun bayyana cewa, Jonathan wanda ya rasa damar koma wa karagar mulki a 2015 a karo na biyu, na samun kira daga magoya bayansa na ya sake fitowa takara a wannan karo. Da yake magana a wata takarda ranar Juma'a, Kakakin jam'iyyar a Legas, Seye Oladejo ya ce abu ne mai wahala a ce tasirin tsohon shugaban ƙasar a siyasance ya iya kada Shugaba Tinubu. Ya bayyana…
Read More

Majalisar Dokoki a Kebbi ta tabbatar da dokar gwaji kafin aure

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dokoki ta Jihar Kebbi tabbatar da dokar yin gwajin lafiya ga masu shirin aure a tsakaninsu a jihar. Ƙudirin, wanda kwamitin lafiya na majalisar ya ɗauki nauyinsa, ya tsallake karatu na ɗaya, biyu da na uku kafin Kakakin majalisar, Muhammad Usman ya tabbatar a ranar Alhamis yayin zaman da suka saba yi a zauren majalisar. Daga cikin ababen da dokar ta ƙunsa akwai tabbatar da yi gwajin ajin jini (genotype) da dangin jini (blood group) a asibitocin da aka amince da su. Wajibi ne kuma a yi gwajin a watanni uku ko sama…
Read More

Sanata Marafa ya fice daga APC

Sanata Kabiru Garba Marafa, tsohon dan majalisar dattawan tarayya daga Jihar Zamfara, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC. Sanarwar haka ta jawo cecekuce a siyasar Zamfara da ma arewacin Nijeriya, ganin matsayin Marafa a jam’iyyar tun kafuwarta har zuwa lokutan da ta samu nasara a jihar. Da yake bayyana dalilan da suka sanya ya yanke shawarar barin jam’iyyar, Marafa ya yi zargin cewa shugabannin APC a matakai daban-daban sun nuna masa rashin adalci. Ya ce, duk da irin rawar da ya taka wajen ganin jam’iyyar ta karfafa gindinta a Zamfara, musamman a lokacin da take da karfin fada a…
Read More

Ƙarin kuɗin fasfo: Ba ku damu da wahalhalun al’umma ba – Peter Obi ga gwamnatin Tinubu

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya caccaki Gwamnatin Tarayyar Najeriya kan ƙarin kudin fasfo da Hukumar Shige da Fice (NIS) ta sanar. A cewar sanarwar NIS, daga 1 ga Satumba, 2025, sabbin farashin fasfo sun kai N100,000 ga takardar shafuka 32 mai ingancin shekaru 5, sai kuma N200,000 ga takardar shafuka 64 mai ingancin shekaru 10. Farashin zai shafi waɗanda ke neman fasfo a Najeriya kawai, yayin da kuɗaɗen wajen kasar suka tsaya a $150 da $230. Obi, cikin rubutun da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana karin kudin a matsayin “tsantsar rashin tausayi” a lokacin…
Read More