Babaji

5698 Posts

BBC ta ƙi karɓar murabus daga editan sashen Hausa, Aliyu Tanko

Gidan yaɗa labarai na Birtaniya, BBC, ya ƙi amince wa murabus ɗin Editan Sashen Hausa, Aliyu Abdullahi Tanko, bayan da ta dakatar da shi na tsawon watanni uku bisa zargin cin zarafi a wurin aiki da wasu tsoffin ma’aikata suka yi. Tanko, wanda aka ruwaito an dakatar da shi a ranar Laraba, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Alhamis, amma hukumar ta ki karɓa. BBC ta gamu da suka sosai bayan wani faifan bidiyo ya yadu, inda tsohuwar ma’aikaciyarta, Halima Umar Salah, wadda ta bayyana a wani shiri a Arewa24, ta yi ikirarin cin zarafi a wurin aiki a…
Read More

Gwamnatin Kano ta bada fili don gina rukunin gidaje a Bichi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin jihar Kano ta bayar da wani katafaren filinta da ke Ƙaramar Hukumar Bichi don gina rukunin gidaje mai guda 2000 wanda Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi zai yi a cikin garin Bichi. Shugaban Majalisar karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya bayyana haka a taron gangamin wayar da kan al'umma da Jami' an Ma'aikatar Raya Karkara da Cigaban Al'umma ta jiha ke gudanarwa a yankunan kananan hukumomin jihar nan, domin sanin abin da jama'a suke bukata da kuma abubuwan dake damunsu, wanda aka yi a sakatariyar…
Read More

Gwamnatin Trump ta janye jami’an farin kaya da ke gadin Kamala Harris

Shugaba Trump na Amurka Donald Trump ya janye masu tsaron tsohuwar mataimakiyar shugaban Amurka a zamanin Joe Biden, Kamala Haris da shugaba Joe Biden ya ba ta, kamar yadda wani daga cikin masu ba ta shawara ya tabbatar. Bisa doka dai a matsayin Kamala na tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasa, ta cancanci samun tsaro na tsawon watanni shida bayan barin mulki a watan Janairu wanda ya kamata ya ƙare a watan Yuli. Tshohon shugaba Joe Biden ya tsawaita lokacin tsaron ga mataimakiyarsa da shekara guda to amma yanzu shugaba Trump ya janye ƙarin a wata takarda da aka yi ranar Alhamis,…
Read More

Ba zan fice ba daga Jam’iyyar NNPP, inji Kwankwaso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi watsi da jita-jitar shirin ficewa daga jam'iyyar, yana mai cewa ya tsayu wajen ganin ya ƙarfafa ta yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027. Da yake jawabi a taron Majalisar Zartarwar jam'iyyar (NEC) a Abuja ranar Alhamis, Kwankwaso ya ce yana sane da jita-jitar da ake yaɗawa cewa zai ɗauki mataki mai ƙarfi game da goben siyasarsa, lamarin da a cewarsa ba gaskiya ba ne. "Bari na yi amfani da wannan damar wajen sanar da ku cewa mu…
Read More

Fenerbache ta sallami Mourinho

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fenerbahce ta kori mai horarawa Jose Mourinho bayan aikin shekara ɗaya da 'yan watanni. Tafiyar ɗan ƙasar Portugal ɗin ta zo ne kwana biyu bayan kulob ɗin ya kasa samun gurbi a gasar zakarun Turai ta Champions League, inda Benfica ta cire su a wasannin neman gurbi. Cikin wata sanarwa, Fenerbahce ta ce Mourinho "ya bar kulob ɗin" kafin daga baya ta gode wa mai shekara 62 ɗin. Daga baya wani jami'i a kulb ɗin ya faɗa wa BBC cewa korarsa suka yi. Mourinho, wanda ya horar da ƙungiyoyi 10 ciki har da Chelsea da Real…
Read More

Ƙarin kuɗin fasfo zai inganta samar da shi, inji Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce tana gudanar da shirye-shiryen ganin ƴan Nijeriya sun samu fasfo acikin mako guda daga sadda suka fara nema. Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bata tabbacin haka yayin bada ba'asin tsakiyar zango na ayyukan ma'aikatar a Abuja, ranar Alhamis. Ya ce, hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen samar wa al'umma fasfo akan lokaci a ƙarƙashin gyare-gyaren da ake yi wa fannin. Hukumar Shige da Fice NIS, ta sanar da ƙarin kaso 100 na kuɗin mallakar fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan…
Read More

Sakkwato: A wani karo, da dama sun rasu a kifewar kwale-kwale

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani hatsarin kwale-kwale da ke maƙare mutane da kayayyaki a yammacin ranar Alhamis ya yi sanadin rasuwar fasinjoji da dama a Ƙaramar Hukumar Shagari da ke Jihar Sakkwato. Mai taimaka wa Gwamna Ahmed Aliyu akan lamuran gaggawa, Aminu Bodinga ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Juma'a inda ya ce an aika da jami'an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA) zuwa wajen da abin ya faru. Ya ce, hatsarin ya auku ne da wani gajiyayyen kwale-kwale a lokacin da ya ɗebo fasinjoji masu yawa tare da kifar da su baki ɗaya. Ya…
Read More

Mai taimaka wa gwamnan Kano, Abdullahi Rogo ya maka mai jaridar Daily Nigeria, Jafar Jafar kotu kan fallasa satar N6.5bn

Wata Kotun Majistare a Kano ta bayar da umarni ga mataimakin sufeton yan sanda mai kula da shiyya ta daya da ya gudanar da cikakken bincike kan zargin wasu laifuka da ake yi wa Jafar Jafar, mamallakin jaridar Daily Nigerian dake Kano. Wannan na zuwa ne bayan karar da Darakta Janar na Mai Kula da Tsare-tsare da tsafiye-tsafiyen Gwamna kano, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, ya shigar a gaban Kotun Majistare ta 15 da ke Nomansland, ƙarƙashin jagorancin Alkalin kotu, Malam Abdul’aziz M. Habib. A cikin ƙarar, Rogo ya tuhumi Jafar Jafar tare da wani Audu Umar da laifin batanci da…
Read More

Editan BBC Hausa, Aliyu Tanko ya yi murabus

Babban Editan sashin Hausa na BBC mafi dadewa, Aliyu Tanko, ya yi murabus, bayan zarge-zargen gallazawa daga tsohuwar ma’aikaciyar gidan, Halima Umar Saleh. Da ya ke tabbatar da murabus ɗin nasa ga manema labarai, Aliyu Tanko ya ce ya yi murabus ne bisa raɗin kansa bayan ya shafe shekaru 17 ya na yi wa BBC hidima cikin kwarewa. Sai dai ya ƙi ƙarin bayani lokacin da DAILY NIGERIAN ta tambaye shi kan zarge-zargen “cin zarafi” daga tsohuwar ma’aikaciyar tashar. Ms Saleh, wadda a yanzu take aiki a matsayin Babbar Editar kafar yaɗa labarai ta TRT Africa, ta bayyana a wata…
Read More

Tinubu ya sanya dokar hana fita da wasu kayan amfanin gona daga Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yunƙuri na bunƙasa masna’antun cikin gida, Shugaba Bola Tinubu ya amince da dokar hana fitar da ƙwallon kaɗanya da ake sarrafawa wajen samar da man-kaɗai har na tsawon watanni shida. Umurnin, wanda zai fara aiki nan take ya biyo bayan rahotannin tafka asara da Nijeriya ke yi sakamakon ficewa da ɗanyar kaɗanyar kafin sarrafawa, lamarin da daƙile kasuwanci da ƙarfafar masana’antun cikin gida. Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, wanda ya sanar da dakatarwar a yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewa matakin zai ƙara darajta kasuwancin man-kaɗai ta hanyar…
Read More