29
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya musanta rahotannin da ke cewa ya jingine shirinsa na tsaya wa takara a zaɓen 2027, inda ya bayyana hakan a matsayin ƙarya mara tushe da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al'umma. Hakan na zuwa ne a lokacin da wani rahoto da jaridar 'Newsweek Nigeria' ta wallafa ya nuna cewa Jonathan ya janye batun tsaya wa takara domin kada ya samar da rarrabuwar kai a kudanci yayin zaɓen 2027. Duk da cewa tsohon shugaban ƙasar bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, alamu masu ƙarfi na nuna…
