Babaji

5698 Posts

Ba ma ɗaukar sababbin ma’aikata, shafin bogi ake yaɗawa – NECO

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Gudanar da Jarrabawa ta Ƙasa (NECO) ta yi watsi da rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tana ɗaukar sabbin ma'aikata, inda ta bayyana hakan a matsayin ƙarya mara tushe da ake amfani da shi wajen yaudarar al'umma. A wata takarda da Daraktan yaɗa labaranta, Azeez Sani ya fitar a ranar Laraba, NECO ta ce ba ta fara ɗaukar ma'aikata ba, kamar yadda ba ta da shirin haka a nan kusa. Ta bayyana cewa saƙon da ake yaɗawa abu ne daga ƴan damfara da ke neman cutar da duk wanda ya…
Read More

Gocewar jirgin ƙasa: Kada irin haka ya sake faruwa – Gargaɗin Tinubu ga NRC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya koka game da gocewar jirgin ƙasa da ya ɗebo fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Talata, lamarin da ya yi sanadin raunata mutane guda shida da tilasta wa Hukumar Kula da Jiragen ƙasa (NRC) dakatar da ayyuka a hanyar. A shafinsa na kafar X, Shugaba Tinubu duk da cewa yanzu yana ƙasar Brazil a wata ziyarar aiki, ya ce ya samu rahoton tsaikon da aka samu a ranar. "Ina bakin ciki da wannan al'amari. Ina addu'ar jimami ga waɗanda suka jikkata, iyalansu, da dukkan fasinjojin da abin ƙuncin ya…
Read More

Yanzu-yanzu: NRC ta dakatar da ayyukan jiragen ƙasa na Abuja zuwa Kaduna kan gocewar jirgi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen ƙasa (NRC) ta dakatar da zirga-zirga a Abuja zuwa Kaduna bayan gocewa da wani jirgi da ke ɗauke da fasinjoji ya yi daga hanyarsa a safiyar yau Talata, lamarin da ya yi sanadin raunata mutane shida. Hakan ya faru ne da misalin ƙarfe 11 bayan jirgin ya tsahi daga Abuja da nufin zuwa Kaduna, inda fasinjojin da ke cikinsa suka razana tare da ficewa daga ciki saboda tsoron kai musu farmaki. Da yake ganawa da manema labarai, Darakta Manaja na NRC, Kayode Opeifa ya ce dakatarwar za ta cigaba…
Read More

Sama da ƙungiyoyin ta’addanci 1,000 ke aiki a Afirka, inji Farfesa Gambari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Wakilin Nijeriya Majalisar Ɗinkin Duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce sama da ƙungiyoyin ƴan ta'adda guda 1,000 ne suke gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na Nahiyar Afirka. Gambari, wanda shi ne shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana haka ne a babban taron jagororin tsaro na Afirka a Abuja, ranar Litinin. Ya ce, ayyukan bincike a Nijeriya sun tabbatar da cewa akwai sama da ƴan ta'adda 1,000 a nahiyar, wanda har zuwa yanzu adadinsu ke cigaba da ƙaruwa. Farfesan ya bayyana cewa, da dama…
Read More

Zargin sauya akalar ₦6.5bn: Ba kumfar baki ake son ji ba, hujjoji za ku gabatar – Tsohon kwamishina ga Gwamnatin Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'amarin zargin sauya akalar Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin Kano na neman ɗaukar wani salo yayin da tsohon Kwamishinan Labarai na zamanin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wato Muhammad Garba, ya zargi gwamnatin jihar da yin kumfar baki wajen yaɗa farfaganda a madadin gabatar da hujjoji. A wata sanarwa da ya fitar wa manena labarai, tsohon kwamishinan ya yi tsokaci game da wata takarda da gwamnatin jihar ta fitar a ranar 25 ga Agusta, 2025 daga Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Ya ce, da fari bai so yin tsokaci akan al'amarin ba…
Read More

ASUU ta yi zanga-zangar lumana bayan rufe jami’o’i

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami'o'in Nijeriya (ASUU) ta gudanar da zanga-zangar lumana a jami'o'in da ke sassan ƙasar bayan Gwamnatin Tarayya ta yi buris da buƙatunta. A baya ne ta sanar da gudanar da zanga-zangar a yau Talata, 26 ga Agusta, 2025 a jami'o'in domin matsa wa gwamnatin kan buƙatunta na samar da walwala da yanayin aiki mai kyau ga lakcarori. A wata sanarwa da ASUU ta fitar ta Shugabanta, Christopher Piwuna, ta ce matakin ya nuna ƙarar yadda suke nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin tarayya da na jihohi suke bayyana rashin damuwa da matsalolin…
Read More

Tinubu ya nemi a kafa ƙungiyar jagororin tsaron Afirka ta dindindin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a samar da ƙungiya ta dindindin ga jagororin tsaro na Afirka a matsayin ɓangare na ƙarfafa haɗakar tsaro tsakanin ƙasashen nahiyar. Tinubu ya bayyana haka ne yayin buɗe babban taron shugabannin tsaro na Afirka a Abuja, wanda aka gudanar a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025. Shugaban Ƙasar, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilce shi, ya ce daga yanzu Afirka ba za ta cigaba da amfani da salo marasa ƙarfi ba wajen daƙile ayyukan ta'addanci, waɗanda suka haɗa da garkuwa da mutane daga ƴan bindiga, sata a…
Read More

Ambaliya: An yi sabon gargaɗi ga wasu jihohin arewa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta gabatar da sabon gargaɗi ga jihohin arewa guda tara sakamakon yiwuwar samun mamakon ruwan sama a tsakanin ranakun 25 da 29 ga watan Agusta, 2025, lamarin da ka iya haddasa ambaliya a garuruwa da dama. Daraktan Reshen kula da lamuran ambaliya da yankuna masu barazanar ambaliya a Ma'aikatar Muhalli, Usman Abdullahi Bokani ya bayyana haka a wata takarda, ranar Litinin a Abuja. A cewar sanarwar, Cibiyar Gargaɗin Ambaliya Akan lokaci (FEW Centre) ta bayyana sassan wasu jihohi a matsayin wuraren da ka iya fuskantar gagarumar ambaliya. Jihohin sune; Adamawa, Bauchi, Borno,…
Read More

2027: PDP ta zaɓi fito da ɗan takarar shugaban ƙasa daga kudu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar jam'iyyar adawa PDP, ta cimma matsayar tsayar da ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 daga yankin kudancin Nijeriya. PDP ta hannun Sakataren yaɗa labaranta, Debo Ologunagba ta sanar da haka a ranar Litinin, yayin taron Majalisar Zartarwarta (NEC) karo na 102 da aka gudanar a Abuja. Ya ce, hakan ya biyo bayan jam'iyyar ta karɓi rahoto daga kwamitin karɓa-karɓa a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Bayelsa, Douye Diri. Ya ƙara da cewa, NEC ta kuma tabbatar da tsarin karɓa-karɓa na Kwamitin Ayyukan jam'iyya (NWC) yayin fuskantar babban taronta a watan Nuwamba. Kwamitin ya…
Read More

Takardun bogi: Gwamnatin Tarayya ta rufe haramtattun manyan makarantu 22

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta fara kulle haramtattun manyan makarantu inda tuni ta rufe kwalejin Ilimi da ba a tantance su ba guda 22 a faɗin Nijeriya. Hukumar kula da Makarantun Kwalejin Ilimi (NCCE) ta ɗauki matakin a ƙoƙarinsu na kakkaɓe ayyukan samar da takardun bogi a fannin ilimi, lamarin da ke barazana ga tsaftarsa acikin al'umma. A wani rahoto da ta fitar, NCCE ta ce ta gano wasu haramtattun kwalejin ilimi guda 22 da ke gudanarwa ba tare da tantance su ko ba su izinin aiki ba. Hakan na zuwa ne ƙasa da mako biyu…
Read More