
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU) ta gudanar da zanga-zangar lumana a jami’o’in da ke sassan ƙasar bayan Gwamnatin Tarayya ta yi buris da buƙatunta.
A baya ne ta sanar da gudanar da zanga-zangar a yau Talata, 26 ga Agusta, 2025 a jami’o’in domin matsa wa gwamnatin kan buƙatunta na samar da walwala da yanayin aiki mai kyau ga lakcarori.
A wata sanarwa da ASUU ta fitar ta Shugabanta, Christopher Piwuna, ta ce matakin ya nuna ƙarar yadda suke nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin tarayya da na jihohi suke bayyana rashin damuwa da matsalolin harkar harkar ilimi a jami’o’in gwamnati.
Daga cikin wuraren da aka yi zanga-zangar akwai: Jami’ar Lagas (UNILAG), Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria; Jami’ar Ibadan (UI), Jami’ar Uyo (UNIUYO), Jami’ar Noma ta Abeokuta (FUNAAB) da sauransu.
Da yake jawabi yakin zanga-zangar, Shugaban ASUU na reshe a UNILAG, Farfesa Idowu Kehinde ya ce idan gwamnatin tarayya ta cika alƙawarin da ta yi wa lakcarorin na ba su haƙƙoƙinsu, babu buƙatar su riƙa dogara da wani kuɗi na aro.
