Hatsari: Jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga hanya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Fargaba da tsoro ya mamaye fasinjoji a safiyar Talata bayan wani jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsarin yin sauka daga kan layi, lamarin da ya sanya fasinjoji da dama tserewa domin tsira da rayukansu. Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya auku ne jim kaɗan bayan jirgin ya baro Abuja da misalin karfe 11 na safe, wanda ya sake tayar da jijiyoyin wuya kan tsaron ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri a ƙasar.

Shaidu sun bayyana yanayin lokacin a matsayin mai cike da firgici da ruɗani, inda mutane ke ihu suna neman hanyar fita. Wani fasinja ya shaida wa Manhaja cewa tsoron aukuwar hari ya ƙara dagula lamarin.

Rahotannin farko sun nuna cewa wasu daga cikin taragon jirgin ne suka ƙwace daga kan layi, abin da ya tilasta tafiyar ta tsaya cak.

Hukumar Nigerian Railway Corporation (NRC) ta tabbatar da aukuwar hatsarin, inda ta bayyana cewa ya faru da misalin ƙarfe 11:09 na safe a kilomita 49 tsakanin tashar Kubwa da Asham. Ta ce an tura jami’an ceto da na tsaro tare da ma’aikatan lafiya don tabbatar da cewa dukkan fasinjojin sun dawo Abuja lafiya. NRC ta kuma roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, tana mai cewa matakan gaggawa sun riga sun fara aiki.

Duk da cewa ba a tabbatar da samun raunuka ko asarar rai ba a lokacin da ake haɗa wannan rahoto, lamarin ya sake tuno da ƙalubalen tsaro da ke addabar hanyar jirgin na Abuja–Kaduna, wanda tun da fari ya kasance mafaka ga matafiya daga hanyar mota mai cike da barazanar garkuwa da mutane.

Iyalan fasinjoji da dama sun riƙa neman ƙarin bayani, yayin da wasu kuma suka bayyana a shafukan sada zumunta suna nuna farin ciki da rashin jikkata da kuma fushi kan sake maimaita irin wannan matsala.

By ukarofi