
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta fara kulle haramtattun manyan makarantu inda tuni ta rufe kwalejin Ilimi da ba a tantance su ba guda 22 a faɗin Nijeriya.
Hukumar kula da Makarantun Kwalejin Ilimi (NCCE) ta ɗauki matakin a ƙoƙarinsu na kakkaɓe ayyukan samar da takardun bogi a fannin ilimi, lamarin da ke barazana ga tsaftarsa acikin al’umma.
A wani rahoto da ta fitar, NCCE ta ce ta gano wasu haramtattun kwalejin ilimi guda 22 da ke gudanarwa ba tare da tantance su ko ba su izinin aiki ba.
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako biyu da Shugaba Tinubu ya ba hukumomin gudanarwa a fannin ilimi umarnin yin tankaɗe wa makarantun domin gano baragurbi daga cikinsu.
Tun da jimawa masu ruwa da tsaki a fannin suke kokawa kan tantance manyan makarantu da ke aiki ta haramtattun hanyoyi.
Lamarin da ke sanya ire-irensu karɓar kuɗaɗen karatu masu rahusa da samar da takardun kammala karatu cikin ƙanƙanin lokaci inda daga bisani ake gano cewa gwamnati da hukumomin ilimi ba su tantance su ba.
