Babaji

5698 Posts

Shari’a ta zama abin sayarwa yanzu a Nijeriya – Sarkin Musulumi ga NBA

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sarkin Musulumi, Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku ya yi gargaɗin cewa shari'a a Nijeriya ta ɗauko hanyar rasa martabarta duba da yadda ta ke fifita masu kuɗi akan talakawa a yayin hukunci. Sarkin ya faɗi haka ne yayin gabatar da jawabi a babban taron Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta 2025 da ake yi a Enugu, ranar Lahadi, wanda masana harkar shari'a da alƙalai da dama suka samu halarta. A cewarsa, rashawa da rashin daidaito sun yi katutu a harkokin shari'a a Nijeriya ta yadda al'umma suke ƙaurace wa cigaba da yarda da samun adalci…
Read More

Tinubu na shirin gabatar wa majalisa kasafin 2026 a Satumba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na miƙa kasafin kuɗin 2026 ga Majalisar Dokoki a watan Satumban 2025 da nufin kawo ƙarshen jinkirin gabatar da shi a ƙurarren lokaci da aka saba yi a baya. Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗaɗe na Tarayya, Tanimu Yakubu ya sanar da haka a takardar ƙididdige adadin kasafi, wadda ke ɗauke da 7 ga Yuli, 2025 a matsayin kwanan wata, kamar yadda PUNCH ta naƙalto daga shafin ofishin a ranar Lahadi. An fitar da takardar ne domin sanar da ministoci, manyan sakatarori, shugabannin hukumomi da wasu manyan jami'an gwamnati…
Read More

ADC ta buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Katsina da Zamfara kan ƙamarin rashin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar adawa ta ADC ta kirayi Shugaba Bola Tinubu da ya sanya dokar ta-ɓaci a jihohin Katsina da Zamfara sakamakon munanan hare-hare da ya yi sanadin rasa rayukan sama da mutane 140 a watanni biyu da suka gabata. A sanarwar da Sakataren yaɗa labaranta, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta bayyana kashe-kashen a matsayin abinda ta kira da koma-baya ga harkar tsaro a Nijeriya, tana mai sukar Gwamnatin Tarayya da gaza samar da mafita a kai. Jam'iyyar ta kuma yi alla-wadai da kisan masallata guda 30 da aka yi a Ƙaramar Hukumar Malumfashi…
Read More

NiMET ta yi hasashen mamakon ruwan sama na kwana uku daga Litinin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama da tsawa a faɗin Nijeriya har na tsawon kwana uku, wato daga ranar Litinin zuwa Laraba. NiMET ta bayyana haka ne ta kafar X, inda ta ce ana tsammanin samun tsawa da matsakaicin ruwan sama a sassan jihohin arewacin Nijeriya da suka haɗa da Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe, da Katsina a safiyar Litinin. A lokacin rana kuma ana sa ran samun ruwan sama a Kebbi, Adamawa da Taraba. Sannan akwai yiwuwar samun matsakaitan ambaliya a jihohin Bauchi, Jigawa,…
Read More

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kebbi, Isa Galaudu ya fice daga jam’iyya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi a ƙarƙashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2019, Sanata Isa Galaudu ya sanar da barin jam'iyyar. Galaudu, wanda ya taɓa zama shugaban ma'aikata na tsohon shugaban Majalisar Dattawa, ya sanar da haka ne a wata takarda da ke ɗauke da 20 ga Agusta a matsayin kwanan wata, sannan ya aika ta zuwa ga shugaban jam'iyyar na Gundumar Augie a jihar. Ya bayyana cewa, ficewarsa daga jam'iyyar za ta fara aiki ne a nan take. Haka kuma, tsohon ma'aikacin na banki kuma tsohon ɗaya daga cikin jagororin Jami'ar Usman Ɗanfodiyo…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Alfred Emberga ya zama Kakakin Majalisar Dokokin Benuwai sa’o’i 48 da Dajoh ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hon. Alfred Emberga ya zama sabon kakakin majalisa a Majalisar Dokoki ta Jihar Benuwai. A yau Lahadi aka rantsar da shi jim-kaɗan bayan da tsohon kakakin, Hyacinth Dajoh ya yi murabus. A safiyar ranar Dajoh ya sanar da yin murabus daga muƙamin a wata takarda, lamarin da ya kai Emberga, wanda ke wakiltar mazaɓar Makurɗi ta Arewa kan muƙamin. Dajoh ya yanke shawarar sauka daga kujerar ne bayan dakatar da mambobin majalisar huɗu da aka zarge su da yunƙurin tsige shi. Waɗanda aka dakatar sun haɗa da Alfred Berger, Terna Shimawua, Cyril Ekong da…
Read More

Katsina: Ƙungiya ta jajenta kisan masallata a masallacin Malumfashi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuj Ƙungiyar Ci-gaban Malumfashi (MADA) ta jajenta wa iyalan waɗanda suka rasu a harin Masallaci da ƴan bindiga suka kai a Gidan Mantau da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a jihar Katsina.Lamarin ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane guda 50. Shugaban ƙungiyar, Malam Salisu Bawa a wata takarda, ya bayyana saƙon ta'aziyyar a ranar Asabar. Ya ce, suna taya iyalan waɗanda suka rasu jimami da kuma fatan samun waraka cikin lokaci ga waɗanda suka jikkata. Bawa ya kuma yi alla-wadai da harin inda ya kirayi gwamnatin tarayya da ta ƙara baza jami'an tsaro a yankunan da…
Read More

Enugu: Obasanjo, Malema da sama da lauyoyi 20,000 sun halarci taron NBA na 2025

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Asabar aka fara gudanar da taron Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta 2025 a Birnin Enugu da aka saba yi a kowace shekara. Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da ɗan siyasar Afirka ta Kudu, Julius Malema da wasu lauyoyi su sama da 20,000 suka samu halarta. Da fari shugaban ƙungiyar, Afam Osigwe ya jagoranci dubunnan lauyoyi a wani zagayen wasa jini a titunan birnin, inda wasu da dama suka riƙa shiga sahunsu daga bisani. Da yake ganawa da manema labarai, Osigwe ya bayyana cewa Enugu waje ne da ke da yanayi mai kyau…
Read More

Takardun kotu sun bayyana yadda direban tirela da wasu ƴan ƙasar waje suka damfari Ɗangote biliyoyin kuɗaɗe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jagoran masu kuɗin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu ƴan kwangila tare da wasu ƴan cikin gida suka kitsa yi masa damfarar maƙudan kuɗaɗe, kamar yadda Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana. Takardun kotu da Sufeton ƴan sanda ya shigar sun bayyana yadda wata tawagar ƴan ƙasar waje suka yi yunƙurin damfarar Matatar Ɗangote kuɗin da adadinsa ya kai Dala miliyan 50. Haka kuma wani direban tirela ya sauya akalar wasu tireloli da ke maƙare da ƙarafunan rodi na kamfanin simintin Ɗangote na wasu biliyoyin nairori. Waɗanda…
Read More

Ba na yunwar zama shugaban ƙasa, inji Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya ce burinsa shi ne Nijeriya ta gyaru, ba manufar kai ta zama shugaba ba. Da yake magana a taron karɓar wasu sababbin mambobin jam'iyyar ADC ranar Asabar a Legas, Atiku, wanda ya samu wakilcin Farfesa Ola Olateju na Jami'ar Achievers da ke Owo, ya ce tafiyar siyasarsa ta ginu ne akan shugabanci na gari da ci-gaban ƙasa. "Shirin Atiku Abubakar shine a gina ingantacciyar ƙasa. Ba wai akan shi a karan kansa ya zama shugaba ko ta wace hanya ba. Abinda aka damu da shi shine a…
Read More