Babaji

5698 Posts

Lafiyarsa lau, hutu ya ke buƙata – Sanata Kalu akan Shugaba Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya yi watsi da batun da ke cewa Shugaba Bola Tinubu yana fama da rashin lafiya kuma an ba shi gado a wani asibitin Birtaniya. Sanatan ya bayyana haka ne bayan sa'o'i 12 da ganawarsa da Shugaban Ƙasar inda ya ce lafiyarsa ƙalau kuma batun da ake yaɗawa ƙanzon kurege ne. Tsohon gwamnan na Abia ya bayyana haka ne a gidansa da ke Maryland a Amurka ta wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook, inda ya ce gajiya ce Shugaban ƙasar ya yi…
Read More

Har yanzu Ɗangote ne wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka – Forbes

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani karo, Alhaji Aliko Ɗangote ya sake kare matsayinsa na wanda ya fi kowane attajiri kuɗi a Afirka, inda ya zama ja-gaba a jaddawalin masu kuɗi na 'Forbes Real-Time Billionaires'. Lamarin da ya sa ya zama na 88 a sahun waɗanda suka fi kowa kuɗi a duniya bayan ya mallaki dukiyar da darajarta ta kai kimanin Dala biliyan 24. A jaddawalin, wanda aka fitar a yau Asabar, ya nuna yadda Ɗangote ya yi fintinkau akan takwarorinsa na Nijeriya, kamar su Abdulsamad Rabi'u mai Dala biliyan 7.2 da Mike Adenuga mai Dala 6.3, sai…
Read More

NITDA ta ankarar da al’umma sabon katin waya da ake damfara da shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Ci-gaban Sadarwa NITDA, ta fitar da saƙon ankara da al'umma game da sabon katin waya da ta gano (eSIM) da ake damfara da shi ta lambobin waya da rajistar data da kutse ga sanarwa gami da yaɗa saƙonnin bogi. A halin yanzu katin ya shafin aƙalla na'urori guda biliyan biyu a faɗin duniya, lamarin da ke ƙara jefa tsaron harkar sadarwa cikin haɗari. A wata sanarwa da ta fitar ga gidajen jarida ranar Juma'a, NITDA ta ce cigaba da yaɗuwar irinsa ka iya shafar biliyoyin salula da sauran nau'ukan na'urorin zamani…
Read More

Hedikwatar Tsaro ta ƙi amincewa da yadda aka fassara kalaman Janar Musa kan kare kai

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta yi karin haske game da kiran da Babban Hafsan Tsaro Janar Christopher Musa ya yi cewa jama'a su fara tunanin koyon dabarun kare kansu da aka amince da su a duk faɗin duniya. Ta ce, jama'a sun yi wa kiran wata fahimta ta daban, to amma abin da babban jami'in tsaron ke nufin shi ne ba wai mutane su dauki makami su kare kansu ba, a'a yana nufin su koyi abubuwa kamar kokowa da judo da dambe da ninkaya da gudu dama tukin mota da dai sauransu. Daraktan yaɗa labaran DHQ, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya…
Read More

Yadda kiran koyon kare kai na Babban Hafsan Tsaro ya ta da ƙura

Yayin da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya shawarci ƴan Nijeriya da su ɗauki matakin koyon kare kai don tsira daga sharin ƴan ta'adda, kalaman nasa sun haddasa cecekuce acikin al'umma musamman a harkokin tsaro, shari'a, ƴancin jinsi da rayuwar yau da kullum. Janar Musa ya bayyana cewa sanin yadda mutum zai kare kansa abu ne mai muhimmanci kamar yadda koyon tuƙi da iyo suke a wajen ɗan-adam. Matar tsohon gwamna a Jihar Ondo , Betty Anyanwu-Akeredolu, ta goyi bayan kalaman babban hafsan inda ta ce ta jima da da buɗe wajen koyon horon faɗan 'taekwondo' ga ƴan…
Read More

Saƙonnin Soshiyal Mediya da ka iya sa a soke bizarka ta Amurka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumomin Amurka sun faɗaɗa hanyoyin tantance sahihancin biza inda suka gabatar da tsarin bincika bayanan kafafen sada zumunta. Rahotanni sun bayyana cewa, daga cikin sababbin dokokin akwai umartar ƴan waje da ke son shiga ƙasar bayyana baki ɗaya kafafen sada zumunta da suke amfani da su na tsawon shekaru biyar da suka gabata daga yanzu. An sabunta tsarin ne da nufin binciken tabbatar da ba a taka dokokin shige da fice ba gabannin bada damar shiga ƙasar. Ƙwararru akan harkar shige da fice sun ce duk wani yunƙuri na ɓoye wata kafa ta Soshiyal…
Read More

Jagoran Boko Haram, Bakoura ya musanta mutuwa a harin sojoji ta sama a Nijar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ibrahim Mahamadou Bakoura, wanda jagora ne na mayaƙan Boko Haram da aka sani da Abu Oumaima ya musanta yana ɗaya daga cikin waɗanda aka halaka a farmakin sojoji. A ranar 15 ga watan Agusta, 2025 rundunar sojoji ta yi ikirarin kashe Bakoura, wanda kuma daɗaɗɗen jagoran ƙungiyar ne na yankin Tsibirin Shilawa dake Kudu maso Gabashin Nijar. Farmakin sojojin ya hari musamman manyan dabobin mayaƙan a yankunan Korongol, Kournawa da Shilawa da ke shiyyar Diffa. A yayin harin ne aka halaka da dama daga cikin mayaƙan, wanda aka ƙaddamar ta sama a yankin da…
Read More

Buratai ya nemi gwamnati ta yi amfani da salon kulle na COVID-19 wajen magance ta’addanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban sojojin ƙasa, Laftanal Janar Tukur Buratai ya kirayi Gwamnatin Tarayya da ta zaɓi salon kulle da aka yi amfani da shi a lokacin annobar COVID-19 domin daƙile ayyukan ta'addanci, ƴan bindiga da garkuwa da mutane a Nijeriya. Da yake jawabi a gidan talabijin na Sunrise Daily ranar Juma'a, Buratai ya ce ƙyale ayyukan ta'addanci su cigaba da wanzuwa abu ne mai haɗari ga Nijeriya da al'ummarta don haka akwai buƙatar a ɗauki matakin da ya dace wajen magancewa. "Za mu iya rufe ƙasar domin tabbatar da kowa ya mayar da hankali kuma…
Read More

Ali Nuhu ya rattaɓa hannu don cimma tsare-tsaren Ma’aikatar Al’adu da Ƙirƙira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tawagar Hukumar Kula da Fina-finan Nijeriya NFC, ƙarƙashin jagorancin Darakta Manajanta, Ali Nuhu, ta halarci taron masu ruwa da tsaki don raya al'adu a Ma'aikatar Al'adu da Ƙirƙira. An gudanar da zaman, wanda aka yi wa take da 'Strategic Repositioning of Nigeria's Art, Culture, Tourism and Economy for National Development and Competitiveness' a ƙarƙashin jagorancin Ministar Ma'aikatar, Barista Hannatu Musawa. Haka kuma, an shirya taron ne na kwana biyu da nufin haɗe dabarun ma'aikatar da manufofin ci-gaban gwamnati wajen faɗaɗa alaƙar hukumomi da samar da ci-gaban ayyuka da tsare-tsaren aiwatarwa. Babban abinda aka cimma…
Read More

Tinubu ya ƙaddamar da na’urar lissafa haraji don ƙididdige kuɗin shiga

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya kirayi al'ummar Nijeriya da su jarraba sabon na'urar lissafa haraji da gwamnatinsa ta ƙaddamar, domin ƙididdige abinda za su riƙa biya a ƙarƙashin sabon tsarin haraji da aka sanya a doka. A wani rubutu ta shafin X ranar Alhamis, Tinubu ya ce na'urar za ta taimaka wa ɗaiɗaikun mutane lissafa adadin kuɗaɗen harajin da ke kansu a sabon tsarin, wanda za a fara aiwatarwa a shekara mai kamawa. Ya kuma ce, tsarin haraji na 'fair tax' ba abu ne da zai magance talauci ba ko ƙara nauyi akan marasa galihu,…
Read More